Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin
Published: 22nd, May 2025 GMT
Ko shakka babu, ba wani tsari ko salon ciyar da al’umma gaba da za a iya cewa zai dace dari-bisa-dari da dukkanin sassan duniya bai daya, amma duk da haka, daukacin kasashen duniya za su iya koyi daga kwarewar kasar Sin, da tsawon lokacin da ta shafe tana gwada dabarunta na ci gaba wadanda suka haifar da da mai ido.
Wasu masharhanta na ganin kwarewar da Sin ke samarwa duniya, tamkar sabon zabi ne ga sassa masu fatan gwada wani salo na bunkasa kasashe masu tasowa, wanda ya sabawa na yammacin duniya, don haka sassa daban daban ke kara rungumar manufofi, da shawarwari da Sin ta gabatar na yin tafiya tare, irin su shawarar “ziri daya da hanya daya”, da hadakar BRICS, da dandalin FOCAC na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da sauransu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp