Duniyarmu A Yau: Kan Tattaunawar Iran Amurka
Published: 22nd, May 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki zamantakewa ysaro da sauransu, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe kuma mu ji ra’ayin masana dangane da su.
///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da tattaunawa tsakanin JMI da kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Wanda ya zuwa yanzu an gudanar zagaye na 4 na tattaunawar. Har zuwa wannan lokacin dai dukkan bangarorin suna fadar cewa ana samun ci gaba a tattaunawar. Amma bayan kwanaki da kammala zagaye na 4, jami’an gwamnatin kasar Amurka sun fito fili sun bayyana manufarsu ta shiga tattaunawa da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Shugaban Trump da kansa ya yi magana haka ma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio shi ma yayi magana inda a fila ya bayyana cewa manufarsu ta shiga tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya itace tabbatar da cewa JMI ta dakatar da tace makamashin Uranium a cikin kasar kwatakwata.
Rubio ya kara da cewa basu hana JMI mallakar cibiyoyi wadanda suka amfani da makamashin nukliya kamar cibiyar gudanar da bincike na Jami’an Tehran don ayyukan binciken magunguna da cibiyar samar da wutan lantarki a Bushar da sauransu ba, amma sai dai iran ta shigo da makamacin daga kasashen waje, amma Amurka ba zata amince Iran ta ci gaba da tace Uranium a cikin kasar Iran ba don kata ta kera makaman nukliya, ko kuma ta wannan hanyarce kawai Amurka zata tabbatar da cewa Iran bata kera makaman Nukliya ba.
Har’ila yau jakadan shugaba Trump na musamman a yankin kudancin Asiya Steve Witkoff ya fadawa kafafen yada labarai da dama kan cewa manufarsu ita ce raba kasar Iran da tace makamashin Uranium daga cikin gida.
Sai dai ganin dukkan wadannan jami’in gwamnatin Amurka sun san cewa wannan ba abin amincewa ne ga JMI ba, Witsoff ya ki kawo wannan batun a dukkan tarurruka guda 4 da suka gudanar da tawagar kasar Iran a Mascat dakuma Roma.
Sannan JMI ta san wanda wannan batun da ma wanda ya fi haka, ta san cewa gwamnatocin kasashen yamma karkashin Jagorancin Amurka suna da matsaloli da dama da JMI wadanda suka hada da matsalar tace Uranium a cikin kasar.
Banda haka suna da tabbacin cewa Iran ba zata kera makaman Nukliya tare da sinadarin Uranium da take tacewa a cikin kasar ba. Abin da yake damun kasashen yamma shi ne Iran tana samun ci gaba na wuce hankali tare da makamashin Uranium da take tacewa a cikin gida a fannonin ilmi da dama.
Don shi makamashin Uranium yana da amfani masu dimbin yawa, musamman a fagen samar da magunguna, ya zuwa yanzu iran ta samar da magunguna da dama wadanda kafin haka sai daga kasashen yamma Amurka ko kasashen turai ake samunsu. Wannan babban hatsarine ga wadannan kasashe wadanda suke mako da wasu ilmi a tsakaninsu don da su ne suke bautar da duniya, don ta su ne suka kashe wanda suka ga dama su raya wanda suka ga dama a duniya.
Wannan shi ne hatsarin da kasashen suke fuskanta daga JMI. Kuma idan baku manta ba a shekarun da ake yi annobar cutar Covit 19 a duniya kasashen yamma sun hana shigowar alluran riga kafin cutar daga kasashensu zuwa JMI. Kuma a lokacin an yi sanda mutane kimani 700 ko fiye da haka suke mutuwa a ko wace rana a kasar Iran sanadiyyar wannan cutar.
Alluran riga kafin cutar Covit 19 na farko da ya shiga kasar Iran itace Sinopham na kasar China, sai Astrazenisca. Amma Amurka take ta sayarwa Iran alluran riga kafin Covit 19, sannan wanda ake shigo da su daga kasashen waje baya isar kasar.
Don haka ne sai masana magungunguna a kasar Iran suka dukufa a cikin yan watanni suka samar da wannan alluran a cikin gida suka wadatar da kasar har All..ya kawo karshen wannan annaoban.
Amma kowa ya ga yadda ma’aikatan Amurka da HKI a cikin kasar Iran suka kashe Dr Muhsen Fakhrzade masanin ilmin kimiyyar sinadarai wanda ya taimakawa kasar ta samar da alluran riga kafin cutar Covid 19. Allura wanda suka bashi sun Fakhar don girmama ayyukansa. Hakan nan kowa ya ga yadda Amurka tare da HKI suka kashe masana fasahar Nukliya a kasar Iran tare da taimakon ma’aikatansu na cikin gida wato Iraniyawa aka kashe Matashi masanin fasahar Nukliya Mustafa Ahmadi Rushan da Dr Muhammadi da sauransu.
Don haka ci gaban kasar Iran a wadannan fasahohi da ilmi suna damun wadanda kasashen wadanda suke son duk duniya ta koma wajensu su kadai don samun wadannan khidimomi na kiwon lafiya da ci gaba.
Makamashin Nukliya tana da amfani masu dimbin yawa, kuma Iraniyawa sun mallaki fasahar sarrafa makamashin nukliya don fiddo da amfaninsa wanda bai da dangantaka da makamin Nukliya.
Amma abinda ya kara munin abun ga kasashen yamma musamman Amurka shi ne JMI taci gaba a makaman zamani, musamman makamai masu linzami wadanda suke sauran fiye da sauran magana ninkin ba ninkin.
Iran wadan nan makamai babu wata garkuwan makamai masu linzamai wacce zata iya tareta da kuma wargazata don haka idan an cillata sai ta sami bararta. Wannan kuma a fili yanke a yakin da HKI take fafatawa da kasar Yemen a halin yan zo. Kasar Yemen wacce take tazarar kilomita fiye da 2000 da HKI amma tana cilla makamai masu linzami samfurin Bilistic su kuma fada a inda suke so a HKI. Kamar yadda ta cilla wasu daga cikinsu wadanda sukafada kan tashar Jiragen sama mafi girma a HKI wato Bengerion a birnin Yafa ko (telaviv).
To kuwa ya san cewa iran tana da iran wadannan makaman don haka ko wadannan kasashe sun shiga yaki da ita ba ita kadai zata ji jiki ba.
Sannan wani abu da yake zuwa tunanin mutane shi ne, wadannan manya-manyan kasashen duniya sun mallaki makaman nukliya ko makaman kissan kare dangi tun karshen yakin duniya na biyu wato a shekara 1945. Kuma Amurka wacce ta fara samun wannan makamin ta yi amfani da wannan makamin kan kasar Japan a karshen yakin. Sannan da wannan makamin ne suka sami nasar a kan Hitala na jamusa da kuma kawayenta aduniya wandaya hada da kasar Japan.
Amurka ta shafe mutane kimani 70000 a cikin yan mintoci a birnin Hiroshima na kasar Japan, sannan haka suka yi a birnin Nagasaki shima a kasar ta Japan.da wadannan makaman ne kawancin kasashen duniya suka sami nasar a kan makiyansu.
Sannan mun san cewa a halin yanzu Amurka tana da dubban irin wadannan makamai wadanda take tsoratar da kasashen duniya da su, haka ma sauran kasashen duniya da suka mallaki wadannan makamai, wato Rasha bayan Amurka dakuma China, sai faransa da kuma ingila ko burtaniya. Kuma idan tura ta kai bongo, sun ga cewa makiyansu sun fikarfinsu da sauran makamai suna iya amfani da wadannan makamai a kan ko wace kasa a duniya don ci gaba da zama a sama, kumamasu karfi a kan kowa a duniya.
JMI bata da makaman nukliya, kuma ta ce bata son mallakar makamin saboda dalilai na addini, daga ciki musulunci bai yadda a yaki a kashe kowa da kowa ba.
To amma JMI zata zauna tana ganin wadannan kasashe masu wadannan makamai masu kissan kare dangi kuma wadanda sub a ruwansau da kashe kowa da kowa, a duniya, musamman ganin abinda HKI take yi a gaza, ya isa misali kan cewa har yanzun za’a iya kashe mafi yawan duniya don su su rayu su kuma ci gaba da iko a duniya. ?
A wannan halin menene JMI ta tanadar don fuskantar makaman nukliyar wadannan kasashe? Idan kaji makaho ya ce muyi wasan dutse to ya san abinda ya taka, ko ya taki dutse. A fili JMI bata bayyana cewa tana da abinda zata tunkari makaman nukliya wadanda kasashen yamma suka malaka ba. Kuma bata taba bayyana cewa ta sami wani makami wanda wargaza makaman nukliya na kasashen yamma ba. Amma kuma mun san cewa dolene ta tanadarwa makaman nukliyar wadannan kasashe.
Don mutane da dama suna cewa ko da ba don ta jefa makamin kan kasashe da birane inda mutane gaba daya suke rayuwa ba, to ta mallaki makamin na nuklkiya mana don tsorarta da makiya. Kan cewa idan sun yi amfani da makaman nukliya a kanat zata rama?
Don haka muna iya cewa yaki yar yaudare ce. Mai yuwa suna da wasu makaman wadanda suki bayyanasu sai ranar da ake bukatarsu. Bamu sani ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya alluran riga kafin makamashin Uranium makamashin Nukliya wadannan makamai wadannan kasashe makaman Nukliya kasashen duniya makaman nukliya kasashen yamma a cikin kasar a kasar Iran wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Za’a Gudanar Da Tattaunawa Zagaye Na 5 Tsakanin Amurka Da Iran A Ranar 23-Afrilu A Roma
Ministan Harkokin wajen kasar Omman ya bada sanarwan cew za’a gudanar da tattaunawa zagaye na 5 tsakanin Iran da Amurka kan shirin Iran na makamshin nukliya a ranar 23 gawatan Mayun da muke ciki a birnin Roma nakasar Italiay.
Tashar talabijin ta Presstv a nnan Tehran ta ce Har yanzun ba’a ji tabakin kasashen biyu ba bayan wannan sanarwan.
Sai dai kafin haka Iran tace tana tunanin dakatar da halattan taron saboda yadda jami’an gwamnatin kasar Amurka suka bayyana cewa duk wata yarjeniya da Iran sai ta hada da hana ta tace Uranium.
Amma iran ta dage kan cewa ba zata bar hakkinta wanda yarjeniyar NPT ta bata ba na tashe Uranium karkashin kula na hukumar IAEA ba.