UNRWA : ba wani abu dake shiga Gaza in banda bama-bamai
Published: 21st, May 2025 GMT
Hukumar Ba da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu a Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar Gaza ta fuskanci matsalar jin kai mafi muni tun watan Oktoban 2023.
A cikin wani sako da ta wallafa a shafin X, UNRWA ta ce yanzu haka makonni 11 kenan da gwamnatin Isra’ila ta hana shigar da abinci, man fetur da magunguna zuwa Gaza.
“Makonni 11, jami’an Isra’ila da gangan sun hana duk wani kayan agaji zuwa Gaza, abin da kawai ke shiga Gaza a yanzu shi ne bama-bamai.
Daruruwan Falasdinawa ne aka kashe a wannan makon yayin da gwamnatin Isra’ila ke kara kai hare-hare ta sama, in ji UNRWA.
“Zafafa hare-haren bama-bamai ta sama da kasa da na ruwa na Isra’ila ya haifar da asarar daruruwan rayuka da kuma gudun hijirar jama’a.”inji hukumar
Mataimakin sakatare mai kula da harkokin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya fada jiya talata cewa jarirai 14,000 a Gaza za su iya mutuwa cikin sa’o’i 48 masu zuwa idan ba a kai musu dauki ba.
Tom Fletcher ya yi Allah-wadai da dokar hana kai kayan agaji zuwa zirin Gaza, yana mai cewa tireloli biyar ne kawai aka ba da izinin shiga a ranar Litinin, wanda ya bayyana a matsayin “digo a cikin teku.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Sake Aiwatar Da Kisan Kare Dangi Kan ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai munanan hare-hare kan Falasdinawa da suka rasa gidajensu da fama da masifar yunwa, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan mutane da dama
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan ‘yan gudun hijira da kuma wadanda ke jiran agaji a zirin Gaza, inda a daren jiya zuwa safiyar Alhamis, hare-haren wuce gona da irinsu suka yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama, tare da jikkata wasu baya ga bacewar wai adadi mai yaw ana mutane a karkashin baraguzan gine-gine.
Asibitin Al-Shifa ya sanar da shahadan fararen hula 11 da suka hada da yara da mata a wani sabon kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata ta hanyar kai hare-haren bama-bamai kan makarantar Mustafa Hafez da ke matsayin mafaka ga ‘yan gudun hijira a yammacin birnin Gaza.
Sannan a wani kisan kiyashi kuma, fararen hula 13 da suka hada da mata da kananan yara ne suka yi shahada a lokacin da jiragen yakin mamayar Isra’ila suka kai hare-hare kan wani tanti da ‘yan uwa Abu Asi suka yi gudun hijira ciki, kusa da masallacin Al-Aqqad da ke unguwar Mawasi a Khan Yunis. Wasu da dama kuma suka jikkata.