Rukunin Karshe Na Alhazan Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
Published: 22nd, May 2025 GMT
Rukunin ƙarshe na mahajjatan Jigawa 368 ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi zuwa Saudiyya don aikin hajjin shekarar 2025.
A wata hira da aka yi da shi a Radio Nigeria kafin tashinsu a daren Laraba, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa rukunin ƙarshe na mahajjatan 368 sun fito ne daga ƙananan hukumomin Birnin Kudu, Buji, da Taura na jihar.
A cewarsa, wannan rukunin ƙarshe ya haɗa da Amirul Hajj na jihar, malamai masu wa’azi, wasu jami’an shiyyoyi da cibiyoyi, da kuma wasu jami’an hukumar.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, jihar ta kammala aikin tantance mahajjata cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.
Ya yabawa Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, bisa goyon baya da haɗin kai da ya bayar ga hukumar.
Darakta Janar ɗin ya kuma yi kira ga sauran mahajjatan Najeriya da ba a ɗauka ba su ƙara haƙuri tare da ci gaba da karanta littattafan da aka basu lokacin bita da shirye-shiryen hajji a jiharsu.
A jawabin bankwana da ya gabatar a filin jirgin sama, Gwamna Umar Namadi ya shawarci mahajjatan da su yi addu’a don jiharsu da ƙasar baki ɗaya.
Namadi ya kuma ja hankalinsu da su bi dokokin da ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa.
Wasu daga cikin mahajjatan da suka yi magana da Radio Nigeria kafin tafiyarsu sun gode wa Allah da ya basu damar zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sun yabawa shugabannin hukumar kula da jin daɗin mahajjata ta jihar Jigawa bisa tanadin abinci da abin sha da suka yi musu yayin da suke sansanin Alhazai da filin jirgi.
Mahajjatan sun bayyana jin daɗinsu da yadda aka tsara wa’azi tare da yabawa jami’an hukumar da yadda suka kula da su a sansanin Alhazai.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa, jami’an hukumar shige da fice, kwastam, da NDLEA ne suka tantance mahajjatan tare da jakunkunansu masu nauyin kilo 8.
Usman Muhammad Zaria.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Uwargidar Gwamnan Zamfara Ta Sake Jaddada Kudurin Dakile Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Jihar
Mai dakin Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta sake jaddada kudurin gwamnatin jihar na ganin an kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.
Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta karɓi shugabannin Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, waɗanda suka kai mata ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Gusau.
Hajiya Huriyya ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da hukumar, domin gano ingantattun hanyoyin da za su taimaka wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar.
“Muna shirin zama tare domin duba hanyoyin da za mu bi wajen magance matsalolin da kuke fuskanta, domin muna da aniyar ganin Zamfara ta nisanta daga illar tu’ammali da miyagun kwayoyi In Shaa Allah.”
Uwargidar Gwamnan ta yaba da jajircewar shugabancin hukumar, tare da tabbatar da cewa ofishinta a bude yake don hadin gwiwa a kokarin inganta rayuwar al’ummar jihar.
Ta kuma taya hukumar murna bisa nasarorin da ta samu a yayin gudanar da aikinta.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Ishaq Anka, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce domin bayyana ci gaban da hukumar ta samu da kuma kalubalen da take fuskanta wajen aiwatar da aikinta.
“A ranar 1 ga watan Maris na wannan shekarar, mun karɓi jimillar mutane 52 da aka kama ana kokarin safararsu. Sojojin Najeriya ne suka cafke su a tsakanin Abuja da Jihar Kogi,” inji shi.
Malam Anka ya bayyana cewa hukumar ta gudanar da gangamin wayar da kai sosai kan illolin amfani da miyagun kwayoyi.
“Mun kuma shirya zaman wayar da kai da manyan limamai a fadin kananan hukumomi bakwai kan illolin amfani da kwayoyi, amfani da su ba bisa ka’ida ba, da kuma barazanar safarar mutane.”
Malam Anka ya bayyana wasu muhimman bukatun hukumar da suka hada da cibiyar gyaran hali, motocin aiki, gidajen kwanan jami’anta, da wasu muhimman kayayyakin aiki.
Daga Aminu Dalhatu