Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano
Published: 21st, May 2025 GMT
Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya (NUEE) reshen Jihar Kano, ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani saboda rashin biyan haƙƙoƙinsu da kamfanin KEDCO ke yi.
Sakataren tsare-tsaren ƙungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Muhammad Babangida ne, ya bayyana hakan a wani saƙon murya da Freedom Radio ta wallafa.
A cewarsa, ma’aikatan KEDCO sun shafe sama da watanni 100 ana cire musu kuɗin fansho daga albashinsu, amma ba a tura kuɗin zuwa inda ya dace ba.
“Tun bayan kafa KEDCO aka fara cire wa ma’aikata kuɗin fansho, amma har zuwa yanzu ba a tura su inda ya kamata.
“Waɗanda suka mutu ko suka bar aiki suna cikin wannan hali, ba a biya su haƙƙinsu ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa duk wani ƙoƙarin da suka yi don sulhu da kamfanin ya ci tura, hakan ya sa suka yanke shawarar shiga yajin aiki.
Ya ce: “Kamfanin KEDCO yana samun kuɗi sosai, amma ya gaza biyan haƙƙin ma’aikata.
“Saboda haka, daga idan mutane sun ga an samu katsewar wuta, ka da su ɗora laifi a kanmu.”
Yajin aikin zai shafi harkokin samar da wutar lantarki a Kano da kewaye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Wutar Lantarki Yajin aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Queen Zeeshaq za ta shiga daga ciki
Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa.
Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu, 2025.
’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano An kashe makiyaya 2 a wani hari a FilatoRahotanni sun nuna cewar a ranar Laraba za a fara bidirin bikin har zuwa ranar Asabar.
An shirya gudanar da walima, ƙwallon ƙafa, saukar karatun Alƙur’ani da sauransu har zuwa ranar ɗaurin aure.
A yanzu matashiyar ta fi mayar da hankali wajen ayyukan jin-ƙan marayu da kuma aikin jarida.
Aminiya ta tuntuɓi makusantan mawaƙiyar don jin dalilin ɓoye bikin, amma sun ce wasu dalilai ne ya sa suka ɗauki wannan mataki.
Matashiyar ta fice a kafafen sada zumunta musamman Facebook, inda ake yin gwagwarmaya da ita kan harkokin yau da kullum.
Ga katin bikin a ƙasa: