Babban Muftin Oman Ya Yi Suka Kan Taron Kungiyar Larabawa Saboda Rashin Saboda Rashin Ba Wa Gaza Muhimmanci
Published: 21st, May 2025 GMT
Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci
Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya jaddada yabonsa ga fitaccen matsayi na kasar Yemen da kuma matsin lamba da dakarun kasar Yemen suke yi na kai kayan agaji a zirin Gaza.
A wani rubutu da ya yi a dandalin X, Al-Khalili ya bayyana godiyarsa ga jaruman kasar Yemen da kuma kasashen da suka bayar da gudumawa wajen matsin lamba don saukaka shigar da kayan agaji Gaza, yana mai cewa, “Ya gode wa Allah da shigar da wasu agajin da aka yi a Gaza,” yana mai jaddada bukatar ci gaba da daukan matakan matsin lamba na kasa da kasa wajen bude mashigar agaji gaba daya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Girmama Shahidan Yakin Kwanaki 12 A Nan Tehran
A jiya laraba ce aka gudanar da taron addu’a da kuma girmama shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka farwa kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taron girmamawan ne a masallacin Imam Khomane (q) da ke nan Tehran.
Labaran ya kara da cewa shahidan yakin kwanaki 12 dai sun hada da manya-manyan sojojin kasar kwamandan dakarun IRGC shahida Hussain salami, da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Shahid Muhammad Bakri da kwamandan rundunar sojojin Khatamul anbiya (s) da ke nan Tehran Ghulam ali Rashti. Da sauransu. Sai kuma masana fasahar makamashin nukliya guda 6 da kuma wasu fararen hula wadanda HKI da Amurka suka kashe a wurare daban daban daga ciki har da yan jarida uku a tashar talabijin ta labarai na farisanci a nan Tehran.