Farar Dabarar Da Tsoffin Masana’antu Ke Yi A Kasar Sin Don Tafiya Da Zamani
Published: 22nd, May 2025 GMT
A bangaren masaku ma, masakar Zhejiang Yingfeng ta samu bunkasar ayyukanta musamman wajen rage yawan abubuwan da ba a bukata domin fitar da kayan da ake sarrafawa da tsafta, bayan ta rungumi amfani da fasahar zamani. Haka nan bangaren rina kaya ya samu ci gaba da kusan kashi 80 zuwa 95 cikin dari.
Bangaren aikin gona shi ma yana samun habaka bisa amfani da fasahohin zamani wajen ayyukan noma, da kula da gonaki, da sayar da amfanin gona da sauransu.
Sashen gudanar da kasuwanci shi ma ba a bar shi a baya ba, inda a shekarar 2024, aka samu cinikin kaya ta manhajar sayar da kayayyaki ta zamani na kimanin yuan biliyan 23.5 a gundumar Ganyu ta birnin Lianyungang dake lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin.
Wadannan tsoffin masana’antun dai na ci gaba da samun bunkasa musamman wajen amfani da makamashi mara gurbata muhalli da fasahar sadarwar mai karfin 5G da kuma rungumar aiki da kirkirarriyar basira domin samun habaka daidai da juyin zamani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa
Hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun daga safiyar yau, sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa da dama tare da jikkatan wasu na daban
Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hulan Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu na daban tun daga wayewar garin ranar yau Talata, sakamakon luguden wuta da jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na zirin Gaza.
Shafin yanar gizo na Palestine Today ya nakalto daga majiyoyin lafiya na cewa: A kalla Falasdinawa 10 ne suka yi shahada sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan makarantar Musa bin Nusair da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar Al-Daraj da ke tsakiyar birnin Gaza.
Wasu 15 na daban kuma sun yi shahada a lokacin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai hari kan gidan mai na Radi a yammacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza.