Wani Mutum Ya Harbe Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Isra’ila A Birnin Washington Na Amurka
Published: 22nd, May 2025 GMT
An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu a birnin Washington na Amurka
Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa: An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu bayan da aka harbe su a wajen dakin adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington D.
Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito sakataren tsaron cikin gida na Amurka na cewa: An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu a kusa da gidan adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington, inda ake gudanar da taron kwamitin Yahudawa na Amurka (AJC). Jim kadan bayan harbin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa an kama wanda ake zargin.
Kamfanin dillancin labarai na NBC ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto jami’ai, cewa wanda ake zargin ya yi harbin yana sanye ne da keffiyeh kuma ya yi ihun “Free Falasdinu” a lokacin da aka kama shi.
Kafofin yada labarai, sun ambato ‘yan sanda, sun bayyana wanda aka kama a matsayin Elias Rodriguez, mai shekaru 30, yana mai cewa “wanda ya yi harbin ba shi da wani tarihin aikata laifuka da zai sa ya zama abin sa ido ga jami’an tsaro.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Yace Yana Jirin Hamas Cikin Sa’o’i 24 Masu Zuwa Don Tsagaita Wuta Na Kwanaki 60
Shugaban kasar Amurka Donal Trump Ya Bayyana cewa nan da kwana guda ko sa’o’ii 24 masu zuwa ne zai sani, ko kungiyar Hamas ta amince da ‘shawararsa ta tsagaita wuta da HKI kuma ta karshe a gaza.
Shafin yanar gizo ta labarai ‘Arabnews ta kasar Saudia’ ta nakalto Trump yana fadar haka a yau jumma’a.
A wani bangare shugaban ya ce yayi magana da gwamnatin kasar Saudia dangane da fadada yarjeniyar Ibrahimia wacce ya samar da ita a shugabancinsa na baya wacce take bukatar kasashen larabawa su samar da huldar jakadanci da HKI, wanda kuma ya sami nasarar a kan wasu kasashen larabawa na yankin tekun Farisa.
Daga shekara ta 2023 ya zuwa yanzu yahudawan sun kashe falasdinawa kimani 56,000 sannan fiye da dubu 12000 suka ji rauni.
Majiyar Falasdinawan ya zuwa yansu, ta bayyana cewa fatansu shi ne tsagait wutar ta kaika ta zamam din-din din.