MDD Ta Nuna Damuwa Akan Tabarbarewar Yanayin “Yan Hijira A Gabashin Kasar Chadi
Published: 22nd, May 2025 GMT
MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su.
Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida.
Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39.
Sanarwar ta MDD ta ci gaba da cewa; Wannan sabon adadin ya karu ne akan wasu ‘yan hijirar miliyan daya da sun dade da shiga gabashin Chadi, tun daga fara yakin basasar Sudan a a tsakiyar watan Aprilu na 2023.
Mai Magana da yawun MDD Stephen Dujarric ya ce; siyasar da kasar Chadi take aiki da ita bude kofofinta ga ‘yan hijirar ne ya bayar da wannan damar.
Haka nan kuma ya bayyana cewa wuraren da aka ware domin tarbar ‘yan hijirar a gabashin Sudan din sun yi kadan’ sannan ya kara da cewa; mafi yawancin masu kwararowar mata ne da kananan yara da su ka kadu saboda yakin da ake yi a can Sudan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Aragchi Ya Musanta Zargin Da Jamus Take Watsawa Dangane sa Shirin Nukliyar Kasar
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi da zancen ministan harkokin wajen kasar Jamus wanda yake cewa, jinginar da aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA wanda JMI ta yi, ya na nuna cewa ba wanda zai bincika ayyukanta na makamashin nukliya ba, kuma ta rufe kofar tattaunawa Kenan.
Aragchi ya bayyana cewa wannan ba haka bane, saboda shirin nukliyar kasar Iran a halin yanzu ya na karkashin majalisar koli ta tsaron kasar Iran ne, don haka ita ce zata fayyece yadda huldar shirin zai kasance tare da hukumar IAEA. Sannan Iran bata fice daga yarjeniyar NPT ba.
Kasar Jamus dai tana goyon bayan hare=hare da HKI da AMurka suka kaiwa JMI a yakin kwanaki 12, dagan cikin harda hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar. Ya ce aiki ne da bai dace ba wacce JKI ta yi madadin kasashen yamma.