Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa Babu Wata Kyakkyawar Fata A Tattaunawar Iran Da Amurka
Published: 21st, May 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ba su tunanin cewa tattaunawar Iran da Amurka za ta haifar da kyakkyawan sakamako
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Iran ba ta jiran izinin kowa wajen inganta sinadarin Uranium, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da manufofinta.
A jiya Talata ne aka gudanar da biki a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) na tunawa da shahadar marigayi shugaban kasa Ayatullah Ibrahim Raisi da mukarrabansa. Bikin ya samu halartar Jagoran juyin juya halin Musulunci, da shugabannin bangarori uku na gwamnati, da manyan jami’ai, da taron iyalan shahidai, da kuma bangarori daban-daban na al’umma.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana a wajen wannan biki cewa: Shahidi Ra’isi bai dauki kansa a matsayin wanda ya fi mutane ba; Ya dauki kansa a matsayi daya daga cikin jama’a, kamar sauran jama’a, har ma kasancewarsa karami fiye da sauran mutane.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Jagoran juyin juya halin Musulunci
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Sojojin Iran ba zasu sararawa Isra’ila ba
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce sojojin kasar Iran ba za su sararawa gwamnatin Isra’ila ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a wani sakon bidiyo ga al’ummar Iran ranar Juma’a biyo bayan hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta yi kan kasar wanda ya kashe fararen hula, masana kimiyya da kwamandojin soji.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta kubuta daga wannan aika-aika ba, yana mai tabbatar wa al’ummar Iran cewa ba za a yi sakaci kan hakan ba.
Jagoran ya jaddada cewa muguwar gwamnatin sahyoniya ta tafka babban kuskure, sannan kuma shelanta yaki ne kan Iran.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: dukkanin jami’an kasar Iran da bangarori daban-daban na siyasa da kuma al’ummar Iran suna da ra’ayi daya dangane da wajabcin daukar wani mataki mai karfi wajen tunkarar gwamnatin sahyoniya ta ‘yan ta’adda.
Jagoran ya kara da cewa, bai kamata gwamnatin Isra’ila ta yi tunanin cewa ta ci bulus ba, kuma komi ya wuce.