Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i.

Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse.

Ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen siyan motoci Sharon guda goma sha shida da kuma motoci Golf Volkswagen guda ashirin domin raba wa mambobin ƙungiyar guda talatin da shida a matsayin tallafin dogaro da kai.

Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma yanke shawarar fitar da wasu karin naira miliyan 431 a matsayin tallafi ga ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa guda hamsin da takwas a fadin jihar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, akwai ƙarin aikace-aikace goma sha bakwai na kudi sama da naira miliyan goma sha tara da ake ci gaba da tantancewa.

Usman Muhammad Zaria.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Neja Ta Jaddada Shirinta Na Yaki Da  Matsalar Tsaro 

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin tsaro a kafatanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar

 

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Mohammad Bello Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a taron shirye-shiryen babban taron tsaro da za a gudanar a Minna.

 

Janar Mohammad Bello Abdullahi ya kara da cewa Gwamnati jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da rashin tsaro, inda ya bukaci hadin gwiwa daga kowane bangare domin cimma burin da aka sanya a gaba.

 

A cewarsa, babban taron zaman lafiya da tsaro na farko da za a gudanar a Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umar Bago, na da nufin hada kai da muhimman masu ruwa da tsaki a fannin tsaro na matakin karamar hukuma, jiha da na tarayya, domin samo ingantacciyar mafita ga kalubalen tsaro a jihar.

 

Janar Bello Abdullahi, wanda ya bayyana kafafen yada labarai a matsayin muhimman masu ruwa da tsaki a yaki da rashin tsaro, ya jaddada cewa sai an hada kai gaba daya ne za a samu nasara.

 

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Jihar Neja, Kwamared Abu Nmodu, ya jaddada cewa akwai bukatar gwamnati ta tantance tsakanin ‘yan jaridu na gaskiya da kuma na bogi, wanda hakan zai taimaka matuka wajen cimma nasarar da ake bukata a jihar, da kuma amfanin al’umma baki daya.

 

Sakataren yada labarai na Gwamnan Jihar Neja, Bologi Ibrahim, wanda Hamza Mohammed mai kula da harkokin yada labarai na Gwamna, ya wakilta, ya bukaci hadin gwiwa domin ci gaban jihar.

 

Taken taron zaman lafiya da tsaro na farko a Jihar Neja wanda za a gudanar gobe Laraba 20 ga watan Mayun 2025, shi ne: “Hadin Gwiwa Wajen Gina Tsaro da Zaman Lafiya Domin Kare Jihar Neja.”

 

Daga Aliyu Lawal

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jihar Neja Ta Jaddada Shirinta Na Yaki Da  Matsalar Tsaro 
  • Maniyatan Jigawa 550 Sun Isa Kasa Mai Tsaki Don Aikin Hajjin Bana
  • Gwamnatin Kano Ta Ƙara Wa’adin Mako Guda Kan Dakatar Da Fina-finai 22
  • Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su
  • Mawaƙan APC sun zargi gwamnati da watsi da su a Jigawa
  • Iyalan Sarkin Da Aka Kama Suna Neman Taimakon Kudin Fanso Shi Miliyan ₦50
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 Sun Raunata 3 A Jihar Kebbi
  • Hajji: Gwamnatin Katsina ta biya wa maniyyata 2000 kuɗin hadaya
  • ’Yan sanda sun ceto tsohuwa mai shekara 80 a hannun ’yan bindiga a Jigawa