Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Karfi
Published: 21st, May 2025 GMT
A bana ake cika shekaru 80 da kawo karshen yakin duniya na II da ma dawowar yankin Taiwan karkashin ikon babban yankin kasar Sin, wadda nasara ce da babu wanda zai goyi bayan lalata ta, sai masu neman cimma wani buri na kansu. La’akari da shekarun da aka shafe, da tsayawar kasar Sin tsayin daka kan tabbatar da iko kan yankunanta, ya kamata yankin Taiwan da masu tunzura shi su fahimci cewa, suna bata lokacinsu domin manufar kasar Sin daya tak, manufa ce da ta samu amincewar kasa da kasa kuma babu wanda zai iya sauyata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatan MDD Masu Kula Da Ayyukan Makamashin Nukliya Na Kasar Iran Su Fice daga Kasar
Hukumar IAEA mai kula da ayyukan makamashin nukliya a kasar Iran ta bada sanarwan cewa ma’aikatan hukumar sun fice daga kasar a jiya Jumma’a bayan da gwamnatin kasar ta jingine aiki da ita, bayan hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa cibiyoyin nuklliya na kasar da ke Fordo, Natanz da kuma Esfahan a yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar.
Hukumar ta bada sanarwan cewa ma’aikatan hukumar a Iran suna cikin kasar a lokacin yakin kwanaki 12 kan Iran, kuma a jiya sun bar Tehran zuwa Vienna bayan da gwamnatin kasar ta jingine aiki da ita, kuma tuni sun isa birnin Vienna inda cibiyar hukumar take.
A ranar Alhamis da ta gabata ne ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragch ya bayyana cewa daga yanzun kuma hukumar zata yi mu’a mala da majalisar tsaron kasa, kan duk wani abu da ya shafi shirin makamashin nukliya na kasar.
Banda haka yace kasar Iran har yanzun bata fice daga yarjeniyar NPT ta hana yaduawar makamashin nukliya ba. Amma hukumar ta bayyana cewa Tehran bata shaida mata a hukumance kan cewa ta jingine aiki da ita ba.
Bayan yakin kwanaki 12, wato a ranar 25 ga watan yunin da ya gabata ne majalisar dokokin kasar Iran ta amince da jingine aiki da hukumar ta IAEA tare da zargin shugabanta Rafael Grossi da zama wanda ya ingiza yakin kwanaki 12 a kan kasar. Sannan yana mika bayanan da ya tattara a iran dangane da shirinta na makamashin nukliya ta zaman lafiya ga HKI.