Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.

 

Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.”

 

Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko, amma yanzu an fara ganin alfanun su, ciki kuwa har da daidaituwar musayar kuɗi, da ƙaruwar kuɗaɗen shiga ga jihohi, da farfaɗowar masana’antun tace mai, da kuma ƙarfafa matsayin kuɗin gwamnati.

 

Yayin da gwamnatin Tinubu take da da cika shekara biyu, ministan ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya suna ganin gagarumin zuba jari da ake yi a harkar ababen more rayuwa, noma, tsaro, da bunƙasa rayuwar ɗan’adam.

 

A cewar sa, an ware naira tiriliyan 2.5 don ayyukan gina manyan hanyoyi a 2025 — adadin da ya fi na kowanne lokaci a tarihin Nijeriya.

 

Ya kuma bayyana ƙirƙirar sababbin ma’aikatu na bunƙasa yankuna da na kiwon dabbobi, domin ƙara bunƙasa arzikin ƙasa da noma da aka yi, da kuma ƙaddamar da shirin lamuni na NELFUND wanda ya taimaka wa ɗaliban Nijeriya sama da 300,000 da kuɗin karatu da gudanar da rayuwar su.

 

Daga cikin sauran muhimman ayyuka da ministan ya lissafa akwai shirin Shugaban Ƙasa na amfani da iskar gas ta CNG a motoci wanda ya jawo zuba jari kai-tsaye na fiye da dalar Amurka miliyan 450; da kafa CreditCorp domin bai wa ‘yan Nijeriya damar samun rance don gina gidajen su da kula da lafiyar su; da kuma ware naira biliyan 200 don tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa, ƙananan sana’o’i (SMEs) da manyan masana’antu.

 

Ya ƙara da cewa: “Yanzu haka Nijeriya ta zama wani gagarumin wurin gine-gine, inda aka kasafta sama da naira tiriliyan 2.5 don gudanar da ayyukan hanyoyi a wannan shekara kaɗai — wanda hakan bai taɓa faruwa ba a tarihin ƙasar nan.

 

“Gwamnati tana haɗa birane ta hanyar manyan ayyuka irin su hanyar Legas zuwa Kalaba da wata hanyar daga Badagry zuwa Sakkwato, da sauran sassa na ƙasa.

 

“Akwai sauran ayyuka da dama da ke gudana yanzu haka. Daga farfaɗowar matatun mai na Fatakwal da Warri, zuwa amincewa da a kashe naira biliyan 80 don sake gina dam ɗin Alau da ke Jihar Borno, zuwa ci gaban aikin gina layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna — babu wani yanki na ƙasar da aka bari a baya a cikin wannan babban zuba jari a ababen more rayuwa ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda yanzu ake kira ‘The Road Master.’”

 

Ministan ya kuma nuna wasu alamomin da ke nuna bunƙasar tattalin arziki inda ya ce, “Ma’aunin Canjin Farashin Kayayyaki (CPI) na watan Afrilu 2025, wanda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta fitar kwanan nan, ya nuna cewa hauhawar farashi ya tsaya a kashi 23.71, wanda an samu raguwar kashi 0.52 daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan bai faru ba sai saboda tsare-tsaren Shugaban Ƙasa, waɗanda yanzu haka sun fara bayyana kuma suna haifar da ɗa mai ido.”

 

Idris ya buƙaci ƙwararrun masanan hulɗar jama’a da su taka rawar gani wajen gina da kuma nuna sabuwar martabar tattalin arzikin Nijeriya ga duniya.

 

“Nijeriya tana bunƙasa!” inji shi. “Nijeriya ta jawo fiye da dalar Amurka biliyan 50 na sababbin hannun jari kai-tsaye daga ƙasashen waje, kuɗin da ‘yan Nijeriya suke turowa daga ƙetare sun kai dala biliyan 21.9, kuma masana’antar finafinai (Nollywood) ta bayar da gudunmawar fiye da naira biliyan 730 ga haɓakar tattalin arziki (GDP).

 

“Waɗannan ba ƙididdiga ba ne kawai — su ne labarai da suke buƙatar a bada su ta hanya mai kyau, bisa ƙwarewa, kuma cikin ƙaunar ƙasa.”

 

Idris ya jaddada cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da inganta saƙonnin ƙasa ta hanyar sabon tsarin sadarwa na ƙasa mai suna National Strategic Communication Framework (NSCF).

 

Ya kuma taya Shugaban Hukumar NIPR, Dakta Ike Neliaku, murna bisa zaɓen sa a matsayin Wakilin Lardi na Musamman (Regional Delegate-at-Large) na ƙungiyar Global Alliance for PR and Communication Management.

 

Ya ce: “Ina taya ka murna, ya Shugaban mu, bisa wannan gagarumar nasara. A ƙarƙashin jagorancin ka, aikin hulɗar jama’a ya samu ƙarin daraja sosai a gida da wajen Nijeriya.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: tattalin arzikin Shugaban Ƙasa

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u 

’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru.

Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda, kuma ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta samu ’yantar da mambobin Cocin Christ Apostolic Church (CAC) 38 da aka yi garkuwa da su a yankin.

Majiyar da ta yi magana da Rediyon Najeriya ta ce ’yan bindigar sun farmaki Aasaru ne a wani daji da ke kan hanyar Koro.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarta, jami’an ’yan sanda daga sashin Eruku sun karɓi korafi a ranar Lahadi cewa wasu mutane huɗu dauke da makamai sun kutsa wata gona a kan hanyar Koro, Eruku, inda suka sace wani Mista Aasanru mai shekaru 40.

Ejire-Adeyemi ta ce ana cigaba da ƙokari wajen ganin an kubutar da manomin da aka sace.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus
  • Tinubu ya gana da Janar Christopher CG Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus
  • Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Yi Murabus
  • Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Ajiye Aiki
  • Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100%
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • Najeriya Ta Kara Ƙaimi Wajen Kawar da Cutar HIV Nan da 2030
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara
  • Olisa Metuh ya sauya sheƙa zuwa APC, ya ce PDP ta manta da shi
  • Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku