Jirgin Karshe Na Alhazan Jihar Kwara Ya Isa Kasa Mai Tsarki
Published: 22nd, May 2025 GMT
Sahun ƙarshe na mahajjata 140 daga jihar Kwara, ciki har da jami’an NAHCON, da ya tashi daga filin jirgin sama na Babatunde Idiagbon da ke Ilori ya isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Yayin jawabi ga mahajjatan kafin tashin su da misalin ƙarfe 6:42 na yammacin Laraba, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar Kwara, Farfesa Mashood Mahmud-Jimba, ya shawarci mahajjatan da su kasance masu ɗabi’a a lokacin da suke kasa mai tsarki.
Farfesa Mahmud-Jimba ya bayyana cewa an shirya duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa mahajjatan sun gudanar da aikin hajji ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma shawarce su da kada su yi ayyuka masu wahala domin samun damar shiryawa yadda ya kamata don gudanar da ibadarsu.
Shugaban ya kuma ja hankalinsu da su yi amfani da cibiyoyin lafiya da aka samar idan suna buƙatar magani.
A nasa jawabin, Amirul Hajj na Jihar Kwara na shekarar 2025, kuma Olupo na Ajase-Ipo, Barista Ismail Yahaya-Alebiosu, ya bayyana jin daɗinsa da irin shirin da aka yi domin jigilar mahajjatan zuwa Saudiyya.
Ya yaba wa gwamnan jihar bisa bayar da goyon baya da kayayyakin aiki ga hukumar domin tabbatar da gudanar da aikin hajji ba tare da tangarda ba.
Barista Yahaya-Alebiosu ya kuma shawarci mahajjatan da su kiyaye dokoki da ƙa’idodi yayin da suke kasa mai tsarki.
A nasa bangaren, Sakataren zartarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya shawarci mahajjatan da su zama jakadun ƙasa nagari.
Ya kuma bukace su da su yi addu’a domin zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin ƙasa yayin da suke a kasa mai tsarki.
Jimillar mahajjata 2,210 daga jihar Kwara ne ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Ali Muhammad Rabi’u
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: gudanar da aikin Jihar Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Kassim: Mayakan Hizbullah Mazajen Fagen Daga Ne
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’ima Kassim ya bayyana cewa; Dakarun Hizbullah mazajen fagen daga ne da ba su karbar kankanci.
Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a wurin babban taron Ashura a ungiyar Dhahiya dake birnin Beirut, ya bayyana cew; Yaki na tsaron kasa zai ci gaba saboda mun yi Imani da ‘yanto da kasa, kuma wajibi ne akansu, ko da kuwa an dauki lokaci mai tsawo sannan kuma sadaukar da kai ya yawaita.”
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Isra’ila abokiyar gaba tana ci gaba da mamaye yankuna 5 na Lebanon, don haka babu yadda za a yi mu mika kai.” Haka nan kuma ya yi tambayar cewa; Ta yaya za a tsammaci za mu ki tsayuwar daka a gaban wannan abokin gfabar wanda yake ci gaba da mamaye kasa da kuma kisa?
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; gwagwarmaya za ta ci gaba, kuma zuriya mai zuwa za su dora daga inda aka tsaya.”
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce: Za mu kare gwagwarmayar da mutane masu yawa su ka sadaukar da kawunansu akanta, domin wannan gwagwarmaya ce ta Imam Musa Assadar, kuma ta Sayyid Hassan Nasrallah shugaban shahidan wannan al’umma.”
Da yake Magana akan yadda HKI take keta wutar yaki, Sheikh Na’im Kassim ya ce; yawan keta wutar yakin Isra’ila ya kai dubban gomomi, ya kuma kara da cewa; Batun da ake yi na wata sabuwar yarjejeniya ba zai sa mu mika wuya ba, abinda ya kamata shi ne a fada wa abokan gaba cewa; Su daina keta wutar yaki, sannan kuma gwgawarmaya tana cikin hanyoyin magance matsalar da ake fuskanta.”