HausaTv:
2025-05-22@21:01:29 GMT

 Nahiyar Afirka Ta Kafa Cibiyar Tattara Bayanai Akan Yanayi

Published: 22nd, May 2025 GMT

Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar.

Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar.

Haka nan kuma cibiyar za ta kyautata ayyukanta ta hanyar harba taurarin dan’adam a sararin samaniya da kafa cibiyoyin bibiyar yanayi domin yin musayarsu da kasashen nahiyar da kuma wajenta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa wasu daga cikin sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su bayanai.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda.

Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON Gwamnati za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta ƙwato a hannun Emefiele 

Ya ce: “Akwai masu bai wa Boko Haram bayanaj a cikin sojoji, ’yan siyasa da sauran jama’a. Za mu ƙarfafa leƙen asiri, kuma mu ɗauki tsattsauran mataki a kansu.”

Gwamna Zulum ya ce dole ne a haɗa kai a yaƙi ta’addanci ta hanyar ƙoƙarin gyara rayuwar al’umma da inganta tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi, ba kawai amfani da makamai ba.

Ya bayyana cewa daga cikin sama da mutum 300,000 da suka miƙa wuya daga ƙungiyar Boko Haram, akwai yiwuwar wasu daga cikinsu sun koma daji.

Ya kuma ce rundunar soji ba ta da isassun kayan aiki da za su iya yaƙar ta’addanci yadda ya kamata, inda ya ce ’yan ta’addan na da kayan zamani sama da na sojoji.

Sai dai ya yaba wa sojojin Najeriya saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen kawo zaman lafiya.

Zulum ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya saurari shawarwarin ƙwararru, musamman sojoji, domin magance matsalar tsaro.

“Dole a kafa jami’an tsaron daji cikin gaggawa. Shugaban ƙasa ya saurari mutane masu gaskiya da fahimtar abubuwa. Ka da a ci gaba da siyasantar da matsalar tsaro,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Modric Zai Bar Real Madrid Bayan Kammala Gasar Cin Kofin Duniya Na Kungiyoyi
  •   Ma’ariv: “Isra’ila” Ta Zama Saniyar Ware A Duniya
  • Boko Haram: Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kafa Sansanin Sojoji A Hong Ta Jihar Adamawa
  • Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan
  • An Tattauna Hanyar Zamanantar Da Kasa A Dandalin Tattaunawa Na Masanan Sin Da Afirka
  • Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum
  • Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar
  • Jagora: Jamhuriyar Musulunci Ba Ta Bukatar Izinin Wani Mahaluki Domin Tace Sanadarin Uranium
  • Kwara Ta Kafa Tutar Hadin Kai Mai Mita 70 A Ilorin