Sojojin Yemen Sun Kai Wa Filin Jirgin Saman “Ben Gorion” Hari Sau Biyu A Yau Alhamis
Published: 22nd, May 2025 GMT
A karo na biyu sojojin kasar Yemen sun sanar da kai hari akan filin saukar jirgin sama na “Ben Gorion” a matsayin ci gaba da taimakawa Falasdinawa da sojojin HKI suke yi wa kisan kiyashi.
Sanarwar ta sojojin na Yemen ta kuma ce; Makami mai linzamin da su ka harba, wanda ya fi sauti sauri ne, kuma ya sauka a inda aka harba shi, wato filin jiragen sama na Yafa dake karkashin mamaya, da ake kira da “Ben Gorion.
Harin ya tilastawa miliyoyin ‘yan sahayoniya guduwa zuwa Mabuya sanadiyyar gittawar makami mai linzamin da aka harbo daga kasar Yemen. Haka nan kuma an dakatar da zirga-zirgar jirage a filin na Ben Gorion.
Da safiyar yau ma dai kakakin sojan kasar ta Yemen Janar Yahya Sari, ya sanar da harba makami mai linzamin zuwa Tel Aviv, da kuma jiragen sama marasa matuki zuwa tashar jiragen ruwa na Haifa.
Janar Sari ya tabbatar da cewa sojojin na Yemen za su ci gaba da kai hare-haren nasu akan HKI har zuwa lokacin da za a dakatar da yakin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar Biliyan ₦2.6bn
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama.
Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye.
Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622, da MLKN01837 – suna nan da inganci kuma sahihai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp