Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin ZamfaraBabu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin Zamfara
Published: 21st, May 2025 GMT
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.
“Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.
“Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda a ƙarshe ta gano cewa ƙarya ce kawai da Sahara Reporters ta ƙirƙira.
“Don tabbatar da gaskiya, gwamnatin jihar ta tuntubi Babban Alƙali na Kotun Shari’ar Musulunci a Zamfara dangane da irin wannan shari’a, inda ya bayyana cewa ba a taba samun irin wannan ƙara a gaban wata kotun shari’a a jihar Zamfara ba.
“Tambayar ita ce, daga ina ne wannan labari mai cike da haɗari da raba kan jama’a ya samo asali? Mene ne dalilin yaɗa shi? Mene ne masu yaɗa wannan labari suke fatan cimmawa a nan gaba?
“Muna rayuwa ne a cikin lokuta masu ban sha’awa. Kafofin watsa labarai da ya kamata su samar wa jama’a da ingantattun labarun suna zama abin kunya, sun zama masu kwafa da watsa labaran bogi don samun mabiya da ‘likes’.
“Matar da aka yi amfani da hotonta wajen yaɗa labaran bogi ba ‘yar Nijeriya ba ce, sunanta Aalia, kuma ‘yar jihar Texas ce ta ƙasar Amurka.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta yi imanin cewa ya zama dole ta fayyace cewa babu wani abu makamancin haka da ke faruwa a jihar.
“Muna kira ga jami’an tsaro da abin ya shafa da su binciki tushen wannan labari na bogi, ba gaskiya ba ne, wanda ke neman haifar da tashin hankali na addini, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotu, dole ne mu ba da gudubmawar mu don tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gwamnatin jihar jihar Zamfara zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
Birgediya Janar Abdulsalam ya roƙi jama’a da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai, duk da cewa rufe kasuwannin na iya kawo wata matsala ga rayuwar yau da kullum.
“Gwamnati na ƙoƙarin ganin an rage tasirin da rufe kasuwannin ka iya haifarwa ga al’umma. Muna roƙon ku fahimce mu saboda zaman lafiya da tsaro,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankunan cewa za a sake buɗe kasuwannin nan ba da jimawa ba, idan aka kammala aikin tsaro da ake gudanarwa.
Kasuwannin da aka rufe suna daga cikin manyan kasuwanni a wannan yanki na Jihar Yobe.
Wani mazaunin Kukareta ya shaida wa wakilinmu cewa ba su san dalilin rufe kasuwannin ba, kawai ji suka yi an ce an bayar da umarni daga sama.
Wani ɗan kasuwa daga Buni Yadi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya ji an ce an rufe kasuwannin ne saboda wasu ’yan kasuwa na sayar wa Boko Haram kayan abinci.
Ya ce, “Ban san da yawa ba, amma abin da na ji shi ne an bayar da umarni a ranar Litinin, suna cewa masu sayar da abinci a waɗannan kasuwanni suna taimakawa Boko Haram wajen siyan kayan abinci.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp