Boko Haram: Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kafa Sansanin Sojoji A Hong Ta Jihar Adamawa
Published: 22nd, May 2025 GMT
Majalisar ta kuma umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da ta samar da kayayyakin agaji ga al’ummomin da hare-haren ya shafa domin bayar da agajin jin-kai.
Da yake gabatar da kudirin, Sanata Abbas, ya ce hare-haren da aka kai sun raba dubban mazauna karamar hukumar ta Hong da gidajensu, tare da lalata musu rayuwa.
Ya yi nuni da cewa, sake bullar ‘yan ta’addan ya zarce Adamawa hat zuwa jihohin Borno da Yobe, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da ke Sipaniya na ƙoƙarin ɗauko Victor Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski wanda ke fama da matsalar raunuka
Ɗan jaridar ƙasar Sifaniya, Gabriel Sans na Mundo Deportivo ya bayyana cewar, Barcelona na neman wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski a matsayin mai jefa ƙwallo a raga, hakan ne ya sa ƙungiyyar ta amince da ɗaukar Osimhen.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFAA ƙarshen kakar bana ne ake tunanin up Lewandowski zai bar Barca, wanda zai tilasta wa ƙungiyyar neman wani zaƙaƙurin ɗan wasan gaba mai ciyo ƙwallo.
Victor Osimhen dai a bazarar nan ne ya koma Galatasaray bayan barin Napoli ta Italiya.
Osimhen dai ba ya ɓoye aniyarsa ta buga wasa a ɗaya daga cikin manyan gasannin Nahiyyar Turai biyar ba, ciki har da Firimiya ta Ingila da LaLiga ta Sifaniya, inda Barcelona ke cikin manyan ƙungiyoyin gasar.