Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho
Published: 21st, May 2025 GMT
Amma kuma kariyar ciniki ba za ta taimaka ga raya sana’o’i da masana’antu a duniya ba. Idan mun lura, a cikin shekaru 10 da suka wuce, yadda kasar Amurka ta dauki matakai na kare sana’o’in samar da karafa, a maimakon ya hana raguwar guraben ayyukan samar da karafa, sai ya haifar da karuwar kudaden da sana’o’i masu alaka suka kashe.
A bangaren kasar Sin kuma, yadda kasar Amurka ke yi mata kafar ungulu don dakile ci gabanta, ya sa wa kamfanonin kasar kaimin gaggauta kirkire-kirkire, don neman tsayawa da kafafuwansu a fannin kimiyya. Idan ba mu manta ba, a farkon bana, kamfanin DeepSeek mai nazarin fasahar kirkirarriyar basira na kasar Sin ya fitar da tsarin R1 da ingancin aikinsa ya kai matsayin na sauran tsarukan AI masu matsayin koli na duniya. Har ma jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ta yi sharhin cewa, babban kuskure ne ga Amurka yadda take neman dakile ci gaban kasar Sin. Abubuwan da suka wakana a tarihi sun shaida mana cewa, ci gaban fasahohi su kan samu ne daga rikici da takara da juna, a maimakon zaman walwala. Ita kuma tsohuwar mukaddashiyar mai mataimaka wa sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Susan Thornton, ta yi nuni da cewa, matakan kayyadewa da Amurka ta dauka, a hakika sun yi matukar samar da kuzari ga kasar Sin ta fannin kirkire-kirkire, inda Deepseek ya shaida hakan. Ta ce, “ba zai yiwu Amurka ita kadai ta mallaki fasahar kirkirarriyar basira ba, kamata ya yi gwamnatin Amurka ta yi watsi da kariyar ciniki da ma kiyayya da take wa kasar Sin, kuma ta yi hadin gwiwa da kasar, don samar da alfanu ga dukkanin bil-Adama bisa fasahar kirkirarriyar basira.”
Ma iya cewa, Madam Susan Thornton mai idon basira ce game da bunkasar sana’o’i masu alaka da fasahar kirkirarriyar basira. Lallai kawo tarnaki ga wasu ba ya kara wa mai yin hakan sauri da kuzarin tafiya. Matakan da kasar Amurka ke dauka na neman dakile ci gaban kasar Sin, ba zai haifar da kome ba, illa su sa kasar ta Sin ta kara karfinta da gaggauta ci gabanta. Sabo da kamar yadda a kan ce, sara da sassaka ba ya hana gamji toho.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA