Salon “Kasa Daya Manufa Daya” Ya Dace Da “Ayyuka Goma” Na Hadin Gwiwa Da Afirka
Published: 22nd, May 2025 GMT
Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a yau Laraba, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar da ke da ruwa da tsaki ya bayyana cewa, aiwatar da matakan da suka dace bisa “Ayyuka guda goma” na hadin gwiwa da Afirka, ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya zuba babban kuzari ga hadin gwiwar Sin da Afirka.
Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, an riga an tattauna tare da kasashen Afirka sau da dama, an kuma amince da tsarin “Kasa daya, manufa daya” wajen tsarawa da aiwatar da matakai.
Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin HunanA karkashin burin habaka kasuwanci, da hadin gwiwar tsarin masana’antu, an fara aiwatar da manufar soke harajin kwastam ga dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe masu karamin karfi, wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da Sin, a ranar 1 ga Disamban shekarar 2024.
Karkashin ayyukan cudanya da juna, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, an kafa ayyukan hadin gwiwar samar da manyan ababen more rayuwa guda 18, wadanda suka shafi fannoni kamar layin dogo, da hanyoyi, da jiragen sama, da wutar lantarki, da kuma sadarwa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA