Hukumar tace fina-finai ta soke lasisin gidajen gala 8 a Kano
Published: 21st, May 2025 GMT
Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta soke lasisin gidajen wasannin gala guda takwas bisa karya wasu dokokinta.
Idan za a tuna a kwanakin baya hukumar, ta soke lasisin wasu gidajen galar bisa samun su da laifin karya dokar hukumar.
Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — ZulumCikin sanarwar da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, ya zayyano wuraren da hakan ta shafa da suka haɗa da Hamdala Entertainment, Lady J Entertainment, Ɗan Hausa Entertainment da Ni’ima.
Sauran sun haɗa da Babangida Entertainment, Harsashi Entertainment, da kuma Wazobiya.
Idan ba a manta ba hukumar a baya-bayan nan ta dakatar da haska wasu fina-finai 22 da suka haɗa da Dadin Kowa, Labarina, Garwashi, Gidan Sarauta da wasu.
Amma bayan wani taron masu ruwa da tsaki na Kannywood an bai wa masu shirya fina-finan wa’adin mako guda don tantance su.
A ranar Talata ma hukumar ta dakatar da yin tallan magungunan gargajiya a cikin fina-finai ko a kan titin har sai an tantance su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Tace Fina finai da Dab I ta Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci.
Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu.
“Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah.
“ Aikin ya wuce batun fannin samar da saukin yin sufurin jiragen ruwan har da tabbatar da an kiyaye janyo matsala ga ayyukan kamun Kifi a hanyoyin na ruwan, “ A cewar Inji Manajar.
Ta kara da cewa, babban shugabanmu na hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne tuni ya riga ya bayar da kwangilar yin aikin, ba wai a jihar Legas kawai ba, har da a sauran hanyoyin ruwa da ke a sassan kasar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA