HausaTv:
2025-06-16@05:49:03 GMT

Sojojin HKI Sun Bude Wuta Kan Jami’an Diblomasiyyar Wadanda Suka Je Jenin

Published: 21st, May 2025 GMT

Sojojin HKI sun bude wuta nag aske kan jami’an diblomasiyya na wasu kasashen Turai wadanda suke kokarin shiga sansanin yan gudun hijira na Jenin don galin yadda rayuwa take tafiya a cikinsa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jamilan diblomasiyya wadanda suke ziyarar sansanin yan gudun hijiran a yau Laraba dai sun hada da jakadun kasashen  Austria, Brazil, Bulgaria, Canada, Chile, China, Masar, Faransa, India, Japan, Jordan, Lithuania, Mexico Morocco, Poland, Portugal, Romania, Rasha, Sri Lanka, Spain, Turkey, tarayyar Turai (EU), da kuma Burtaniya.

  Tare da su akwai wakilai daga wasu kasashen duniya da kuma yan jarida.

Ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin Falasdinawa ne ta shiryawa wadannan kasashen ziyara zuwa wannan yankin na yamma da kogin Jordan don ganewa idanunsa yadda HKI ta maida rayuwan falasdinawa a yankin yamma da  kogin Jordan da aka mamaye.

Ma’aikatar ta aiwatar da irin wannan ziyarar zuwa sansanin yan gudun hijira na  Tulkaram da ke yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye.

A wasu hotunan bidiyo da aka nuna, an ga yadda wasu jami’an diblomasiyya suke nuna fushinsu da yadda sojojin yahudawan sukabude masu wuta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Kakkabo Jiragen Yakin Isra’ila Biyu Kirar F-35

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta harbo jiragen saman yaki kirar F-35

Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta yi nasarar harbo jiragen yaki kirar F-35, bayan da ta yi nasarar auna wasu jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kirar F-35 guda biyu, kuma ta barar da su kasa.

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da wadannan jirage masu tsananin ci gaban zamani wajen kai hare-haren wuce gona gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da safiyar ranar Juma’a, wanda hare-haren suka yi sanadiyyar shahadar wasu manyan jami’an sojan Iran da masana kimiyyar nukiliya da fararen hula da suka hada da mata da kananan yara.

Ma’aikatar hulda da jama’a ta rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Dakarun tsaron saman Iran sun harbo jiragen saman yaki kirar F-35 guda biyu, baya ga wasu jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya marasa matuka ciki.

Sanarwar ta nuna cewa: Jami’an tsaron Iran sun kame daya daga cikin matukan jiragen wacce mace ce, kuma ana kan bincike domin sanin makomar matukin daya jirgin.

Abin lura shi ne cewa: Jiragen yakin kirar F-35 da ‘yan sahayoniyya ke amfani da su na daga cikin wadanda suka ci gaba a duniya kuma ake gwada su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Cilla Makamai Kan HKI Da Rana A Karon Farko A Yau Lahadi
  • Dakarun IRGC Sun Kakkabo Jirahen Yakin HKI Wadanda Ake Sarrafasu Daga Nesa A Lardin Zanjan
  • Kakakin Gwamnatin Iran Ta Ce daga Yau Lahadi Wuraren Fakewa A Bude Suke Sa’o’I 24 A Tehran
  • Yadda wani ɗan sanda ya rasu a hanyar zuwa ɗaurin aurensa
  • HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina
  • Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi
  • Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Kakkabo Jiragen Yakin Isra’ila Biyu Kirar F-35
  • Jagora: Sojojin Iran ba zasu sararawa Isra’ila ba
  • Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin
  • An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu