Gaza : Birtaniya ta dakatar da tattaunawar cinikayya da Isra’ila
Published: 21st, May 2025 GMT
Birtaniya ta dakatar da tattaunawar cinikayya cikin ‘yanci da Isra’ila, bayan firaminista Keir Starmer ya ce ya kadu da yadda Isra’ila ke ci gaba da yakin Gaza.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ya bayyana matakin jingine batun ciniki tsakanin Birtaniya da Isra’ila, ya kuma nemi jakadan Isra’ila a Birtaniya ya bayyana a gaban Ofishin Lamurran Cikin Gidan kasar domin ya amsa tambayoyi game da yakin da kasarsa ke ci gaba da yi a Gaza.
Mista Lammy ya ce ministan da ke lura da lamurran da suka shafi gabas ta tsakiya na Birtaniya, Hamish Falconer, zai sanar da Hotovely cewa, “hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza har na tsawo makonni 11 mugunta ce kuma babu hujjar yin hakan” .
” A yanzu muna ci gaba da shiga wani mummunan yanayi game da wannan yaki” in ji shi.
Lammy ya kara da cewa yakin da ake yi a Gaza ya haifar da nakasu ga alakar da ke tsakanin Birtaniya da Isra’ilan, sannan ya ce gwamnatin Birtaniya za ta sa takunkumi ga mutane uku ‘yan Isra’ilan wadanda ke da hannu wajen tayar da mazauna Gaza daga muhallansu.
Wannan na zuwa ne bayan da rundunar sojin Isra’ila ta sanar a makon da ya gabata cewa za ta zafafa kai hare-hare a Gaza.
A wani lamari da za’a ce irinsa ne na farkoA ranar Litinin, a cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen Canada, Faransa, da Birtaniya sun yi Allah wadai da fadada yakin da Isra’ila ke yi a Gaza tare da yin kira ga gwamnatin kasar da ta dage takunkumin da ta hana shigar da kayayyakin jin kai a Zirin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa
Hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun daga safiyar yau, sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa da dama tare da jikkatan wasu na daban
Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hulan Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu na daban tun daga wayewar garin ranar yau Talata, sakamakon luguden wuta da jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na zirin Gaza.
Shafin yanar gizo na Palestine Today ya nakalto daga majiyoyin lafiya na cewa: A kalla Falasdinawa 10 ne suka yi shahada sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan makarantar Musa bin Nusair da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar Al-Daraj da ke tsakiyar birnin Gaza.
Wasu 15 na daban kuma sun yi shahada a lokacin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai hari kan gidan mai na Radi a yammacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza.