Aminiya:
2025-05-22@23:54:46 GMT

Ba mu tilasta wa kowa ya koma APC ba – Tinubu

Published: 23rd, May 2025 GMT

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki masu cewa gwamnatinsa na ingiza ’yan Najeriya wajen bin tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa ba za ka iya zargi mutane kan zaɓar jam’iyya ba.

Da yake jawabi a wajen taron ƙoli na jam’iyyar APC  karo na farko da aka yi a ranar Alhamis, da ya gudana a fadar shugaban ƙasa a Abuja, shugaban ya ce “jam’iyya ɗaya ce ke mulki”.

Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe 

“Ga waɗanda har yanzu suke tunanin fita daga jam’iyyarsu, ƙasar nan taku ce, ku riƙe ta, ga masu maganar tsarin jam’iyya ɗaya, jam’iyya ɗaya ce ke mulkin Najeriya, ba za ku zargi mutanen da ke shirin ficewa a jam’iyyar ba.

“Na yi farin ciki da abin da muke da shi kuma ina tsammanin ƙari. Haka lamarin yake. Muna cikin tsarin mulkin demokraɗiyya.”

Ya ce, babu wanda zai iya tilasta wa kowa ya tsaya a inda bai so, ya ƙara da cewa APC a shirye take ta karɓi ƙarin ’yan Najeriya da ke son shiga jam’iyya mai mulki.

Ya ce, “Suna ganin jam’iyyar siyasa ta gaza, amma da jajircewarku, ba mu yi ƙasa a gwiwa ba, mu ne masu ci gaba, za mu yi sojan gona, ku ci gaba da yin aiki tuƙuru… Ina saurarenku ba su ba.

“Muna da damar da za mu sa Afirka ta kasance mai mai ci gaba, amma ina roƙonku da a ci gaba da tafiya tare. Ga waɗanda ba zan iya ba ma muƙaman siyasa ba, ku yi haƙuri, za ku yi farin cikin shiga wannan jam’iyya.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Tottenham ta lashe Gasar Europa bayan doke Manchester United

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta zama zakarar Gasar Europa bayan doke Manchester United da ci ɗaya mai ban haushi.

Tottenham ta kafa tarihi a yau Laraba na lashe kofi tun bayan shekara 17 da ta lashe wani babban kofi.

Zargin Satar Fasaha: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar BBC Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum

Ƙungiyar ta samu nasara ne ta hannun ɗan wasan gabanta, Johnson a minti na 42 kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Ƙungiyoyin biyu sun kara da juna ne a daren ranar Laraba a filin wasa na San Mamés da ke ƙasar Sifaniya.

Hakan na nufin Manchester United ta ƙare kakar wasa ta bana ba tare da ta lashe kofi ko ɗaya.

A yanzu haka Manchester United na matsayi na 16 a gasar Firimiyar Ingila, yayin da Tottenham Hotspur ke biye mata a matsayi na 17.

Gasar Firimiyar Ingila ya rage wasa ɗaya kacal a kammala, wanda tuni Liverpool ta lashe gasar makonni biyu da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Ayyuka Ta Bayyana Nasarorin Tsakiyar Zango Karkashin Shirin “Renewed Hope” na Shugaba Tinubu
  • Ma’aikatar Tsaro Ta Fitar da Rahoton Nasarori Karkashin Shirin “Sabuwar Fata” na Shugaba Tinubu
  • Tottenham ta lashe Gasar Europa bayan doke Manchester United
  • Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON
  • Jigajigan Jihar Kebbi Sun Bukaci Hadin Kan ‘Ya’yan Jam’iyyar APC
  • Iran ba ta jiran izinin kowa kan tace uranium, Dole ne Amurka ta daina maganar banza_Jagora
  • ’Yan bindiga: Zamfara sun koma kwana a jeji
  • An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin maniyyata a Saudiyya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kula Da Lafiyar Jikinku