An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe
Published: 22nd, May 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta sanar da samun nasarar kuɓutar da wata mace mai shekara 22 da aka yi garkuwa da ita tare da kama wasu mutum biyu.
An kama mutum biyun ne da ake zargi da alaƙa da wani mummunan hari a ƙauyen Tashan Randa da ke ƙaramar hukumar Fika.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce samamen da aka gudanar tare da haɗin gwiwar mafarautan yankin, ya nuna wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da rundunar take yi na yaƙi da rashin tsaro a jihar.
Sanarwar ta ce, a ranar 6 ga Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 5:58 na yamma, wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki gidan Maikudi da ke ƙauyen Tashan Randa, inda suka yi awon gaba da ’yarsa tare da raunata wata yarinya maƙwabciyarta da harbin bindiga.
Sanarwar ta ƙara da cewa, jami’an rundunar sun gaggauta gudanar da bincike, inda suka yi amfani da buƙatar kuɗin fansa da ake nema ₦5,000,000 domin gano masu garkuwa da mutanen.
“An kama wasu mutane biyu, Waiti Bello mai shekara 30 daga ƙauyen Jangalawaje da Idrissa Adamu mai shekara 35 na ƙauyen Biriri, ƙaramar hukumar Gujba, dukkansu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, kuma suna taimakawa wajen gudanar da bincike.
“An samu nasarar gano bindigar toka guda ɗaya da babur da aka yi amfani da su wajen kai harin.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Yobe, CP Emmanuel Ado, ya tabbatar da ƙudurin rundunar na kawar da munanan laifuka.” Muna ci gaba da jajircewa wajen kare al’ummarmu.
Wannan nasarar ta nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da ’yan ƙasa,” inji shi, inda ya buƙaci mazauna yankin da su bayar da rahoton abubuwan da ake zargi ga rundunar don magance lamurra kafin su kasance. Cewar CP Emmanuel.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar.
Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa.
Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara yi.
Yankuna da dama a Nijeriya musamman a Arewa- Maso- Yamma, Arewa- Maso- Gabas da Arewa ta tsakiya sun zama lahira kusa a bisa ga yadda barayin daji ke garkuwa da mutane, kone garuruwa da yi wa jama’a kisan kare dangi.
Gagarumar matsalar wadda tuni ta zama tamkar ruwan dare a tsayin shekaru ta ci dimbin rayuka da dukiyoyin al’umma ba adadi ba tare da samun gagarumar nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma ba.
Masana tsaro sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan sauye- sauyen. Wasu na ganin cewa sabbin jini za su iya kawo canji, yayin da wasu suka yi gargadin cewa sauya shugabanni kadai ba zai wadatar ba idan ba a yi gyaran tsari ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA