‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Sun Kammala Aiki A Wajen Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin
Published: 23rd, May 2025 GMT
‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin dake cikin da’irarta, sun kammala jerin ayyukansu na farko a wajen tashar a yau Alhamis.
Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta ce, ‘yan sama jannatin da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun yi aiki na tsawon sa’o’i 8, inda suka kammala da misalin karfe 4:49 na yamma agogon Beijing, bisa taimakon takwarorinsu dake duniyar dan Adam.
Chen Dong da Chen Zhongrui ne suka yi aiki a wajen tashar, inda suka fita ta hanyar dake jikin kumbon Tianhe. Wannan shi ne karo na farko da ‘yan sama jannati suka fita ta hanyar tun bayan da tashar ta shiga matakin gini da na aiki da bincike.
‘Yan sama jannatin sun kuma kafa na’urar kare tashar daga burbushin sararin samaniya a inda ya kamata. A baya, hannun mutum-mutumin inji ne ya kafa na’urar na wani lokaci na wucin gadi. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.
Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.
Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.
Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.
Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.
Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp