Iran ba ta jiran izinin kowa kan tace uranium, Dole ne Amurka ta daina maganar banza_Jagora
Published: 21st, May 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce iran ba ta bukatar izinin kowa kan inganta sinadarin urenium din ta, don haka Amurka ta daina maganar banza da dagewa akan wannan batu inji shi.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa, babban kuskure ne a ce su (Amurka) ba za su bari Iran ta inganta sinadarin Uranium ba.
Ayatullah Khamenei ya bayyana shakkunsa game da sakamakon tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin bikin tunawa da zagayowar ranar shahadar tsohon shugaban kasar Ibrahim Raisi.
A lokacin mulkin shahid Raisi, an gudanar da shawarwari irin haka da Amurka, amma ba a kai ga cimma wani sakamako ba, inji shi, Don haka, ba ma fatan wani sakamako daga wadannan shawarwarin, kuma ba mu san abin da zai biyo baya ba.”
Ayatullah Khamenei ya yaba da irin tsayin dakan da Raisi ya yi, yana mai jaddada cewa bai taba barin makiya su iya tilastawa Iran zama kan teburin tattaunawa ta hanyar barazana, matsin lamba ko yaudara ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kuma yi karin haske dangane da dagewar da Amurka da sauran kasashe suka yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta inganta sinadarin Uranium ba.
“Tabbas, zan bayyana wa al’ummar Iran daga baya dalilin da ya sa suka dage kan batun inganta sinadarin Uranium.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: inganta sinadarin Khamenei ya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Rattaba Hannu Kan Daftarin Dakatar Da
Hadin Gwiwa Da Hukumar IAEA
Shugaban kasar Iran ya rattaba hannu kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, bisa wata doka da Majalisar Shawarar Musulunci ta kafa kwanan nan
Sanannen abu ne cewa: Wannan doka ta zo ne bayan hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, a daidai lokacin da Iran ke shirin tunkarar tattaunawar nukiliya karo na shida da Amurka!
Har ila yau, an san cewa shawarar ba ta zama ficewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi ba, a’a, ta dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ce ta IAEA har sai an cika wasu sharudda, musamman tabbatar da tsaron cibiyoyin makamashin nukiliya da masana kimiyya na Iran.
Harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, cin amanar diflomasiyya ce, da yarjejeniyoyin kasa da kasa, da dokoki. kuma wata mummunar yaudara ce da Trump ya cimma da hadi baki da Netanyahu don tauye hakkin Iran don kai harin. Da wannan ne Trump, wanda Netanyahu da jiga-jigan ‘yan sahayonyiya suka tunzura shi a Amurka, ya dauki matakin yin mummunar illa ga kima da martabar Amurka a duk duniya.