Tottenham ta lashe Gasar Europa bayan doke Manchester United
Published: 22nd, May 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta zama zakarar Gasar Europa bayan doke Manchester United da ci ɗaya mai ban haushi.
Tottenham ta kafa tarihi a yau Laraba na lashe kofi tun bayan shekara 17 da ta lashe wani babban kofi.
Zargin Satar Fasaha: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar BBC Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — ZulumƘungiyar ta samu nasara ne ta hannun ɗan wasan gabanta, Johnson a minti na 42 kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Ƙungiyoyin biyu sun kara da juna ne a daren ranar Laraba a filin wasa na San Mamés da ke ƙasar Sifaniya.
Hakan na nufin Manchester United ta ƙare kakar wasa ta bana ba tare da ta lashe kofi ko ɗaya.
A yanzu haka Manchester United na matsayi na 16 a gasar Firimiyar Ingila, yayin da Tottenham Hotspur ke biye mata a matsayi na 17.
Gasar Firimiyar Ingila ya rage wasa ɗaya kacal a kammala, wanda tuni Liverpool ta lashe gasar makonni biyu da suka gabata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Firimiyar Ingila Gasar Europa Kwallon Kafa matsayi Zakara Kofi
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin Iyakar Thailand da Cambodia Ya Tilasta wa Dubban Mutane Barin Muhallansu
Jami’ai sun ce mutane sama da dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari.
Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna.
Dubban mutane ne suke guduwa domin tserewa lugudan makaman roka da ake harbawa daga Cambodia.
Kazalika Thailand ma na ci gaba da kai wa Cambodia hare-hare ta sama.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana kyautata tsammanin zai gana da shugabannin kasashen biyu ta wayar tarho, wanda ya matsa musu lamba aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yulin da ya gabata.
To sai dai ministan harkokin wajen Thailand ya gargadi Amurka akan amfani da wata barazana ko haraji domin tursasa komawa teburin sulhu don cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
bbc