Sojojin Sudan Sun Gama Tsarkaka Birnin Khartoum Daga ‘Yan Tawayen Rapid Support Forces
Published: 21st, May 2025 GMT
Sojojin Sudan sun karbe iko da sansanin dakarun kai daukin gaggawa na karshe a birnin Khartoum fadar mulkin kasar
Sojojin Sudan sun ci gaba da dama a jihohin Kordofan da Darfur, inda suka bar birnin Nahud da ke yammacin Kordofan, wanda sojojin suka killace birnin ta kowane bangare.
Sojojin Sudan sun samu nasarar karbe ikon yankin Atrun mai mahimmanci a Arewacin Darfur, tare da bude hanyar shiga sauran garuruwan Darfur gaba daya.
Bayan kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a yankin Al-Saliha da ke kudancin Omdurman, wanda ya dauki tsawon sama da wata guda ana gwabzawa, sojojin sun samu nasarar mamaye yankin gaba daya, sai dai wasu kananan yankuna da sojojin ke hadawa, a cewar kakakin rundunar sojin Sudan.
Rundunar kungiyar Rapid Support Forces ta dakaraun kai daukin gaggawa ta mayar da martani ta hanyar kai hari a wani ma’ajiyar makamai a tsakiyar Omdurman tare da wani jirgin sama maras matuki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Da Tawagarsa Sun Isa Kasar Brazil Don Halartar Taron BRICS Karo Na 17
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tafi kasar Brazil don halartar taron BRICS karo na 17
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya sanar da isar ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Rio de Janeiro domin halartar taron kasashe mambobi a kungiyar BRICS karo na 17.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tawagar kasar Iran karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi za ta halarci taron kasashen BRICS.
Baqa’i ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: “Sun isa birnin Rio de Janeiro na Brazil, domin halartar taron kasashen BRICS karo na 17.”