Falasdinawa 94 sun yi shahada a Hare-haren Isra’ila a rana guda
Published: 21st, May 2025 GMT
Bayanai daga Zirin Gaza ne cewa mutane 94 ne sukayi shahada a bayan hare-haren sakamakon harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a zirin a cikin kwana guda.
Adadin ya karu sosai a baya ga kusan mutane 60 da kafafen yada labarai na Falasdinu suka sanar.
Isra’ila ta kai hare-haren ne kan gidaje, makarantu, da matsugunai da dai sauransu.
Alkalumman shahidai sakamakon hare-haren na Isra’ila tun soma yakin a watan Oktoban 2023 ya kai akalla 53,573, akasari mata da kananan yara.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Saudiyya Ya Ɗauki Nauyin Falasɗinawa 1,000 Su Sauke Faralin
Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila.
Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin.
Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da HezbollahSarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke ciki sakamakon yaƙi da ƙasar Yahudawa ta Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp