Tattalin Arziƙin Nijeriya Na Ƙara Farfaɗowa – Gwamnan CBN
Published: 21st, May 2025 GMT
A baya-bayan nan, Bankin Duniya ya ce tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙaru da kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2024, alamar cewa tattalin arziƙin na farfaɗowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.কীওয়ার্ড: Cardoso Farfaɗowa Tattalin Arziƙi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ƙaddamar da wani babban kwamitin ƙirƙiro masarautu da gundumomin hakimai a jihar.
An ƙaddamar da kwamitin ne a wani mataki na magance buƙatu da dama daga al’ummomi daban-daban da kuma inganta al’adu da tsarin mulki na asali a faɗin Jihar Bauchi.
Abba ya naɗa Ahmed Musa a matsayin Babban Manajan Kano Pillars An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a BornoGwamna Bala ya shaida wa kwamitin da ya sake duba buƙatu na samar da sabbin masarautu a faɗin jihar.
Ya ce, aikin kwamitin shi ne inganta harkokin gudanar da mulki na cikin gida da inganta al’adu da kuma ƙarfafa muhimmiyar rawar da sarakuna ke gudanarwa wajen haɗin kai da ci gaba.
Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin alƙawarin da gwamnatinsa ta yi na tabbatar da adalci da haɗa kai da kuma ƙarfafa tsarin mulki da ci gaba a Jiha da ƙananan hukumomi.
Ya bayyanawa kwamitin da ya ba da shawarar al’ummomin da suka cancanta na sabbin masarautu, da ba da shawarar tsarin gudanarwa don ingantaccen aiki na sabbin masarautu, masarautu ko gundumomi da gabatar da cikakken rahoto tare da shawarwari masu dacewa cikin makonni takwas.
Gwamnan ya buƙaci kwamitin da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da himma da kuma adalci.
Ya bayyana cewa, shirin na cika alƙawuran siyasa ne da nufin karkatar da hukumomi don samar da ingantattun ayyuka da kuma ƙara rarraba albarkatu.