Sanata Mai Wakiltar Kebbi Ta Tsakiya Ya Raba Kayayyakin Tallafi
Published: 22nd, May 2025 GMT
Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Sanata Muhammad Adamu Aleiro, ya raba wa al’ummar mazabar sa kayan tallafi da nufin ba su damar dogaro da kai.
Kayayyakin sun hada da babura 150 (Keke NAPEP), babura 114, firiza mai zafin rana guda 302, injin nika 750, famfunan ruwa mai amfani da hasken rana 500, injin dinki 800 da kuma buhunan taki 3,400.
Da yake jawabi a wajen bikin raba kayayyakin a karamar hukumar Aleiro ta jihar Kebbi, Sanata Adamu Aleiro, ya ce hakan na daga cikin romon dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa kadai, har ma da jihar.
Sanata Aleiro, ya lissafo wasu ayyukan da ya aiwatar a matsayin aikin mazabu a kananan hukumomi takwas na mazabarsa da suka hada da hanyoyi, lafiya, ilimi, kawar da zaizayar kasa da kuma cibiyoyin koyon sana’o’i.
Ya shawarci gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasiru Idris, da ya ci gaba da daukar muhimman ayyukan titunan gwamnatin tarayya a jihar, yana mai tabbatar da cewa a matsayinsu na ‘yan majalisa za su bi diddigin irin wadannan ayyuka domin ganin gwamnatin tarayya ta biya kudaden da aka kashe.
Shima da yake jawabi a wajen rabon kayayyakin, Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasiru Idris, ya yabawa Sanatan bisa yadda yake barbade al’ummarsa da ribar dimokuradiyya.
Gwamna Idris, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin sa ba ta taba hana wani dan majalisa damar samar da ayyukan mazabu ga jama’arsa ba yana mai cewa, duk wani aiki da za a kawo a Kebbi don amfanin al’ummar Kebbi ne.
Ya bukaci wadanda suka amfana da kada su sayar da kayayyakin, su yi amfani da su domin dogaro da kai.
COV/Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu
Amma ya nuna damuwa cewa jinkiri wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ASUU na ƙara haifar da rashin jituwa.
Ya roƙi Shugaba Tinubu, da ya sa baki kai-tsaye don kawo ƙarshen rikicin, yana mai gargaɗin cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki na iya gurgunta ci gaban da aka samu a fannin ilimi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA