Modric, ya lashe kofuna 28 da suka hada da gasar zakarun Turai 6 da Laliga 4 tun lokacin da ya koma Real daga Tottenham a shekarar 2012.

 

“Na zo ne a shekarar 2012 tare da fatan sanya rigar yan wasan da suka fi fice a duniya da kuma burin samun manyan nasarori, Real Madrid ta canza rayuwata a matsayina na dan wasan kwallon kafa da kuma mutum, ina alfahari da kasancewata a daya daga cikin mafi kyawun kulob a tarihi” inji shi.

 

Real za ta bude gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa da Al-Hilal ta Saudi Arabiya a ranar 18 ga watan Yuni, sannan kuma za ta kara da Pachuca ta Mexico da RB Salzburg ta Austria a matakin rukuni.

 

Modric ya ci kwallaye biyu sannan ya taimaka aka ci shida a wasanni 34 da ya buga a gasar ta Sifaniya a kakar wasa ta bana, yayin da Barcelona ta lashe gasar.

 

Wasan na ranar Asabar, shi ne na karshe da Ancelotti zai jagoranci Real, inda aka ruwaito kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso  zai maye gurbin kocin dan kasar Italiya, shugaban kulob din Florentino Perez. A cikin wata sanarwa da ya fitar yana cewa, “Modric zai kasance har abada a cikin zukatan dukkan Madridistas a matsayin dan wasan kwallon kafa na musamman kuma abin koyi wanda a ko da yaushe ya kasance yana kunshe da kimar Real Madrid.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan 

A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na kasar Sin masu daraja. (Fa’iza Mustapha)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Wutar Lantarkin Da Sin Ke Iya Samar Ta Amfani Da Karfin Ruwa Ta Kai Matsayin Koli A Duniya
  •  Nahiyar Afirka Ta Kafa Cibiyar Tattara Bayanai Akan Yanayi
  •   Ma’ariv: “Isra’ila” Ta Zama Saniyar Ware A Duniya
  • Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan
  • Tottenham Ta Doke Manchester United A Wasan Karshe Na Europa 
  • Bayan Shekaru 42 Babu Kofi, Tottenham Ta Lashe Gasar Europa League Akan Manchester United 
  • Bayan Shekaru 42, Tottenham Ta Lashe Gasar Europa League Akan Manchester United 
  • Tottenham ta lashe Gasar Europa bayan doke Manchester United
  • Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan