Zargin Satar Fasaha: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar BBC
Published: 21st, May 2025 GMT
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 3 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan shari’ar BBC da mawaƙi Abdul Kamal.
Tunda farko Abdul, ya maka kafar ne a kotu, inda yake neman ta biya shi diyyar Naira miliyan 120, kan zargin amfani da waƙarsa a shirinsu na “Daga bakin mai ita” ba tare da izininsa ba.
A zaman shari’ar na ranar Litinin, lauyan mai ƙara, Barista Bashir Ibrahim Umar, ya gabatar da makaɗin waƙar, Muhammad Sani Uba a matsayin ɗaya daga cikin shaidun wanda ke ƙara.
Makaɗin ya tabbatar wa kotu cewa shi ne, ya yi wa Kamal kiɗan da ake shari’ar a kansa.
Daga bisani alƙalin kotun, ya sanya ranar 3 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan shari’ar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Ƙara Wa’adin Mako Guda Kan Dakatar Da Fina-finai 22
An shirya sake zama a ranar Alhamis mai zuwa don kammala tattaunawar gaba ɗaya.
Cikin waɗanda suka halarci ganawar har da wakilan MOPPAN kamar su Abdul Amart, Nazifi Asnanic, da Abubakar Bashir Maishadda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp