Majalisar Wakilai Za Ta Gabatar Da Dokoki Biyar Don Gyara Bangaren Man Fetur
Published: 21st, May 2025 GMT
Majalisar Wakilai za ta gabatar da kudurori guda biyar da za su magance manyan kalubale da ke hana ingantaccen aiki a harkar man fetur ta kasa.
Shugaban kwamitin Majalisar kan Albarkatun Man Fetur, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na hadin gwiwa da kwamitin musamman kan matsalar satar danyen mai a Abuja.
Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya ce kudurorin da ake shirin gabatarwa, za a gabatar da su ne tare da shugabannin kwamitocin biyu, kuma wani bangare ne na matakan dokoki don tallafawa kokarin gwamnati wajen kare kadarorin man fetur da gas da kuma dakile matsalar satar danyen mai.
Ya bayyana cewa daya daga cikin kudurorin na neman kafa Hukumar Kasa da za ta sami ikon dakile ayyukan masu lalata bututun mai da gurfanar da su , da kuma aikata wasu laifuka da suka shafi bangaren man fetur.
“Kwamitocin da duk Majalisar baki daya na matukar damuwa da karuwar rashin tsaro da ayyukan laifi a yankunan da ake hakar mai. Wannan mataki na majalisa wata hanya ce ta tallafa wa kokarin gwamnati wajen kare wadannan muhimman kadarorin kasa,” in ji Alhaji Ado Doguwa.
Har ila yau, Alhaji Ado Doguwa ya bayyana cewa daya daga cikin kudurorin da ke karkashin Kwamitin Albarkatun Man Fetur (Sashen Sama), wanda Kakakin Majalisar, Dr Abbas Tajuddeen, ke jagoranta, na neman kafa Hukumar da za ta kula da cire kayan aikin hakar mai da suka tsufa, matsala da ke da matukar muhimmanci ga al’ummomin da ke karbar bakuncin ayyukan man fetur da sauran masu ruwa da tsaki.
Salihu Tsibiri
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ayyukan ‘Yan Ta’adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci
Gwamnatin Nijeriya na da shiraruwa da dama da manufar wadata kasa da abinci, inganta samun kudin shiga a karkara da rage fatara ta hanyar shiraruwa masu dorewa na bunkasa aikin gona, sai dai a kodayaushe kalubalen ‘yan ta’adda na hana shiraruwan samun nasara.
Rahotanni da dama sun ruwaito yadda ‘yan ta’adda ke tilastawa manoma biyan haraji gabanin su ba su damar shuka da girbe amfanin gona a gonakin su wanda hakan babban kalubale ne ga manoma da kasa bakidaya.
A bisa ga kasa biyan harajin da barayin dajin ke tilasta masu, dimbin manoma sun rasa rayukan su wasu kuma da dama sun yi gudun hijira daga garuruwan su domin tsira da rayukan su.
A watan Yuni da ya gabata kadai jagoran ‘yan ta’adda, Bello Turji ya bayyanawa manoma za su iya noma ne kawai cikin kwanciyar hankali idan suka biya harajin naira miliyan 50.
Kudin fansar da ya kakaba masu ya shafi manoma ne a tsallaken Gulbi daga kauyen Fakai a karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara zuwa Kaya bakin iyaka da kasar Nijar.
Biyan haraji tuni ya riga ya zama tamkar al’ada ga manoma a wuraren da ke da hatsarin ‘yan ta’adda a Arewa domin su samu damar gudanar da shuka da girbi ba tare da wata matsala ba.
Duk da haka a lokutan baya rahotanni sun tabbatar da rasa rayukan manoma da dama bayan biyan harajin a yayin da a wasu lokutan suke rasa amfanin gona ga ‘yan ta’addan ko kuma a yi biyu babu bakidaya.
Bincike ya nuna bukatar ‘yan ta’addan ta fi kamari ne a jihohin Zamfara, Neja, Katsina, Kaduna, Sakkwato da Benue a inda manoman kan hadu da fushin ‘yan ta’addan idan suka sabawa umurnin su ta hanyar kona amfanin gonar tare da kai masu hari a garuruwan su.
A bisa ga wannan jama’a da dama sun watse a garuruwa da dama a bisa ga kasa iya biyan harajin da barayin dajin suka tilasta masu wanda gudun hijira ne kadai mafitar tsira da rayukan su.
Wani manomi kuma shugaban al’umma a Katsina da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewar harajin da barayin dajin ke saka masu a wasu lokutan yana da yawan da babu riba idan aka hada da abin da suka shuka wanda a kan hakan manoman da ke fuskantar barazanar ke kauracewa gonaki.
“Akwai mamakin sanya harajin naira miliyan biyar ga manomin da gonar sa ba za ta kai miliyan biyu ba kuma a mafi yawan lokuta akan hada manoma da yawa a sa masu biyan harajin. Harajin da za ka biya a wasu lokutan ya danganta da yanayin abin da ka shuka. Kisa ne hukuncin rashin biya tare da lalata amfanin gonar da kai mana kazamin hari.”
Ya ce hare- haren ta’addanci da barayin daji ke kaiwa a gonaki tare da lalata amfanin gona da aka girbe na kara sanya damuwa kan makomar kasar nan wajen samar da wadataccen abinci.
Ta’addancin wanda kai tsaye ake kaiwa ga amfanin gona ya kara bayyanar da kasawar Nijeriya a fannin noma ta hanyar saka miliyoyin jama’a a cikin barazanar yunwa. Da yawan manoman da suka fuskanci kalubale gabanin kammala noma, kan hadu da kunar zuciya yayin cire amfanin gona.
Kafafen yada labarai sun ruwaito yadda ‘yan ta’adda suka kunnawa masarar da aka cire wuta a kauyen Kwaga da unguwar Zako duka a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna tare da barin manoman cikin mawuyacin hali.
Ire- iren makamancin wannan harin da ‘yan ta’adda ke kaiwa a gonaki su kone amfanin gona bakidaya bayan an riga an girbe a na shirin kaiwa gida da kasuwa ba bakon abu ba ne ga manoma musamman a yankin Arewa.
A damanar da ta gabata daga Arewa ta tsakiya zuwa Arewa maso- yamma an samu munanan rahotanni kan yadda hatsabibin ‘yan ta’addan ke gallazawa manoma ta hanyar kone gonakin gero, masara, dawa da wake da sauran amfanin gonar da aka riga aka yi girbi wanda ya girgiza gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan aika- aikar da ta faru tuni Majalisar Dinkin Duniya a karkashin shirin ta na samar da abinci da shirin duniya na samar da abinci da ma’aikatar gona da samar da abinci ta tarayya da sauran abokan hulda suka yi hasashen cewar mutane miliyan 33 a jihohi 26 da Birnin Tarayya za su fuskanci karancin abinci a tsakanin Yuni da Agusta wannan shekarar 2025.
Jihohin da hasashen ya bayyana zai shafa sune Kaduna, Zamfara, Sakkwato, Borno, Adamawa, Yobe, Gombe, Taraba, Katsina, Jigawa, Kano, Bauchi, Filato, Kebbi da Neja.
A yayin da gwamnati ke kashe makuddan kudade domin ganin ta samu nasarar wadata kasa da abinci, a kuma daidai lokacin da ‘yan ta’adda ke yi wa shirin zagon kasa babban nauyin da ke kan gwamnati shine daukar kwararan matakan yakar ayyukan ta’addanci da dukkan karfin ta domin samar da zaman lafiyar da za ta baiwa al’umma sukunin yin noma da wadata kasa da abinci a cikin kwanciyar hankali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp