Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Ce; Gwamnatin Siriya Zata Iya Rugujewa Cikin ‘Yan Makonni
Published: 21st, May 2025 GMT
Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwaryar Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makonni
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwarya a Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makwanni, lamarin da zai sa kasar ta fada cikin yakin basasa matukar Amurka ba ta ba ta hadin kai ba.
A yayin zaman Majalisar Dattijan Amurka, Sakataren harkokin wajen kasar Rubio ya yi furuci da cewa: Idan Amurka ta yi aiki da gwamnatin Siriya, yana iya yiwuwa, gwamnatin ta samu nasara, ko kuma gwamnatin ta kasa samun nasara idan Amureka ba yi aiki da ita ba, kuma tabbas ba zata taba samu nasara ba.
Ya kara da cewa: “A hasashen Amurka, idan aka yi la’akari da kalubalen da ake fuskanta, gwamnatin rikon kwaryar Siriya “watakila a ‘yan makwanni, ba watanni ba, da yiwuwar durkushewarta da kuma bullar yakin basasa, wanda gaba daya zai haifar da wargajewar kasar.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fransa Ta Kira Yi Kasashen Turai Da Sake Bitar Alakarsu Da “Isra’ila”
Ministan harkokin wajen Faransa ya kira yi tarayyar turai da ta sake bitar alakarta da Isra’ila saboda ci gaba da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Gaza da kuma hana shigar da kayan agaji.
Matakin na Faransa dai ya biyo bayan na kasashen Spain, Ireland da kuma Holland, da suke son ganin an gudanar da bincike akan ko hare-haren Gaza din sun karya wani sashe na yarjejeniyar tasu. A karkashin yarjeniyoyin tarayya a tsakanin turai da HKI da akwai batun kare hakkin bil’adama.
Tun a cikin watan Yuni na 2000 ne nahiyar turai din ta kulla yarjejeniyar ayyuka a tsakaninta da HKI a fagage da dama, da hakan ya bai wa Tel Aviv fifiko na musamman a cikin kasuwannin turai. Harkokin kasuwanci a tsakaninsu ya kai dala biliyan 46.8 a 2022.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya bayyana cewa; Saboda matsayar Isra’ila akan gaza, ya zama wajibi a yi bitar alakarta da tarayyar turai.
Barrot ya bayyana tsananta hare-haren akan Gaza da kuma hana shigar da kayan abinci da cewa ” Ba abu ne da za a lamunta da shi ba.”
Haka nan kuma ya bayyana hare-haren na Isra’ila da cewa; cin zarafin Karaman dan’adam ne da kuma keta dokokin kasa da kasa, kuma yana cin karo da tsaron Isra’ila da Faransa ta yi alkawalin karewa,to amma duk abinda mutum ya shuka shi zai girba.
Gabanin Faransa, Faransa, kasar Holland ta yi kira irin wannan na yin bitar alaka da Isra’ila,wacce ministan harkokin wajen na Faransa ya ce, yana goyon baya.