Arsenal Na Dab Da Daukar Dan Wasan Gaba Viktor Gyokeres
Published: 21st, May 2025 GMT
Kungiyar Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting CP, Viktor Gyokeres kamar yadda jaridar wasanni ta football365 ta ruwaito.
Arsenal ta fuskanci matsalolin ‘ƴan wasan gaba a kakar wasan da ke dab da ƙarewa, yayin da ƙungiyar ta gaza lashe kowane irin kofi.
Bayan ƙarewa a mataki na biyu a Gasar Premier da samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai ta baɗi, a yanzu hankalin ƙungiyar ya karkata kan samun ɗan wasan gaba, domin sake gina kanta.
A ƙarshen kakar wasa da muke ciki ne Gyokeres ɗan asalin Sweden zai bar ƙungiyar Sporting bayan ƙarewar kwantiraginsa, kamar yadda Fabrizio Romano fitaccen ɗan jaridar wasanni ya bayyana a shafinsa na X.
BBC
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.
Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11.
Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu.
NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuA kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan