Gwamnatin Afirka Ta Kudu Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Turawa ‘Yan Kasar Fararen Fata
Published: 22nd, May 2025 GMT
Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu
Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata.
An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai.
A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika wasu takardu da alamu ke da alaka da wadannan zarge-zarge.
Ramaphosa dai ya nuna natsuwa a lokacin da yake mayar da martani kan zargin, yana mai cewa manufofin gwamnatinsa gaba daya sun yi hannun riga da abin da Trump ya fada.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kwamitin AU: Kasar Sin Aminiya Ce Da Za A Iya Dogaro Da Ita
Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Mahamoud Ali Yousouf ya yabawa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar AU cewa, kasar Sin a matsayin aminiya ce da za a iya dogaro da amincewa da ita.
A yayin da yake karbar takardar wakilcin kasa daga sabon shugaban tawagar jakadun kasar Sin dake kungiyar AU Jiang Feng, Mahmoud Yousouf ya bayyana cewa, kungiyar AU tana son karfafa mu’amala da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, domin samar da tabbaci ga kasashen duniya dake fama da sauye-sauye a halin yanzu.
A nasa bangare kuma, Jiang Feng ya mika gaisuwa da fatan alheri na shugabannin kasar Sin ga shugaba Yousouf, ya kuma yaba wa kungiyar AU bisa babbar gudummawar da ta bayar ga aikin shimfida zaman lafiya da zaman karko a nahiyar Afirka, da jagorantar dunkulewar kasashen Afirka, da kuma yin kira da a nuna adalci ga kasashen Afirka da sauransu. Haka kuma, ya ce kasar Sin tana son hada kai da kungiyar AU wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing, tare da gina makomar al’ummomin Sin da Afirka ta bai daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp