Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Ce; Ba Ta Gaggawar Neman Kulla Alaka Da Kasar Siriya
Published: 22nd, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda alaka da Iran za ta iya taimakawa al’ummar Siriya, a shirye mahukuntan Iran su amsa bukatar ta.
A wata hira da tashar talabijin ta Al Sharq, Araqchi ya jaddada dimbin damammaki, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi wajen kulla kyakkyawar huldar makwabtaka da yankin da ke kewaye, kuma Iran ta bi ta wannan hanya.”
Ya kara da cewa: “Iran ta kulla alaka mai kyau ta fuskar siyasa, tattalin arziki da al’adu tare da dukkan makwabtanta da kasashen da ke kewaye, Iran makwabciya ce da Siriya kuma kasashen biyu suna zaune a yanki guda tsawon dubban shekaru.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Da Tawagarsa Sun Isa Kasar Brazil Don Halartar Taron BRICS Karo Na 17
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tafi kasar Brazil don halartar taron BRICS karo na 17
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya sanar da isar ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Rio de Janeiro domin halartar taron kasashe mambobi a kungiyar BRICS karo na 17.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tawagar kasar Iran karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi za ta halarci taron kasashen BRICS.
Baqa’i ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: “Sun isa birnin Rio de Janeiro na Brazil, domin halartar taron kasashen BRICS karo na 17.”