2025-10-27@11:45:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1676
«Goyon Bayan»:
Gwamnatin kasar Colombia ta bada sanarwan cewa sojojin Amurka wadanda suke cikin ruwan tekun Carabian sun shiga ruwan yankin kasar kuma sun kashe wani mai kama kifi a itasayen da suke yi a cikin tekun don hana abunda suka kira yaki da safarar miyagun kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran IP ya nakalto...
An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin...
’Yan Sanda sun saki ɗan jaridar Kano, Ibrahim Ɗan Uwa Rano, bayan tsare shi da suka yi kan zargin ɓata sunan hadimin Gwamnan Jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo. An tsare Rano a Shiyyar ’Yan Sanda ta Ɗaya da ke Kano, bisa zargin ɓatanci. Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku ’Yan sanda sun tsare ɗan...
A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci. Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar...
Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Ruguza Gaza “ba abin da za a gaskata ba ne” domin an rusa yankin gaba daya Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai, Tom Fletcher, ya ce: Girman barnar da aka yi a zirin Gaza abu ne da ba za a taba mantawa...
“Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar. A cewar rundunar sojoji, an gano...
Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta bai wa mutanen garin Buhari da ke Karamar Hukumar Yunusari a Jihar Yobe, tallafin Naira miliyan 23 tare da alƙawarin gina rijiyar ruwa mai amfani da hasken rana. Wannan tallafi ya biyo bayan wani harin kuskure da jiragen yaƙin rundunar suka kai a watan Satumba 2021, wanda ya yi sanadin...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala. Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman Sayyid Abdul-Malik Badreddin al-Houthi ya yi jawabi a yammacin yau alhamis kan batutuwa daban-daban da suka shafi duniyar musulmi, musamman abubuwan da suka faru a Gaza da Yemen. Ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ba tare da la’akari da duk wani matsin lamba ba, ta yi...
Jakadan Amurka na Musamman kan Harkokin Larabawa da Afirka, Massad Boulos, ya ƙaryata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya babu gaira babu dalili. Ya ce hare-haren ta’addanci da ke faruwa a ƙasar suna shafar Kiristoci da Musulmai baki ɗaya. An rantsar da Randrianirina shugaban Madagascar Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun...
An rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin Madagascar, bayan ya jagoranci hamɓarar da shugaba Andry Rajoelina. Sabon shugaban Madagascar kuma ya jaddada cewa hawan sa, ba juyin mulki ba ne, domin ya samu goyon bayan kotun tsarin mulkin ƙasar. Gwamnonin APC sun yi taro a Jihar Kebbi ’Yan sanda sun...
Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka
Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta...
Zanga-Zangar Miliyoyi A Yemen Ta Jaddada Alkawari Ga Shahidai Da Ci Gaba Da Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu
Zanga-zangar miliyoyin mutane a birnin Sana’a na sabunta alkawarin da aka yi wa shahidai tare da tabbatar da shirin tallafawa Falasdinu Babban birnin kasar Yemen, Sana’a, ya halarci wani tattaki na miliyoyin mutane a yau Juma’a mai taken “Shekaru biyu na bayar da gudummawa… da aminci ga jinin shahidai”, tare da tabbatar da gwagwarmaya na...
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana...
Saboda haka, an samu labari daga bangaren Obi cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa ba za yi zaben fid da gwani ba da Atiku. Sai dai kuma, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ki cewa uffan kan jita-jitan da ke cewa jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zaben fid da gwani, wanda...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima October 17, 2025 Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin...
Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da KuraAfuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da Kura
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin...
A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkatar mutane da dama. Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata. Hare-haren sun shafi garin...
Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki. Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa. Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar...
Ya ce kamar ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da FAO ke takawa a bangaren aikin gona da samar da abinci a duniya. An kafa hukumar FAO ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 1945, kuma Sin na daya daga cikin kasashe mambobi...
Kungiyar Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da...
Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar. Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin,...
Wani daga cikin waɗanda suka ji rauni, wanda shi ne mai kuɗin, ya gode wa jami’an FRSC bisa gaskiya da amana da suka nuna, yana mai cewa abin koyi ne ga kowa. FRSC ta gargaɗi direbobi da su riƙa kula da motoccinsu akai-akai tare da bin ƙa’idojin hanya domin guje wa aukuwar haɗura. ShareTweetSendShare MASU...
Hukumomi a Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar taƙaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, sannan za ta ɗan dakata ta buɗe bakin iyakar zirin daga Rafas. Isra’ila ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira jan ƙafa da a cewarta Hamas ke yi wajen mayar da sauran...
Hukumar Kula Da GIdajen Gyaran Hali A Zamfara Ta Neman Shigarda Fursunoni Tsarin Inshorar Lafiya Na NHIS
Kwanturola na hukumar gyaran Hali a Najeriya reshen jihar Zamfara, Murtala Muhammad Haruna, ya yi kira da a shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIS) domin tabbatar da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya. Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga kwamishiniyar lafiya ta jihar...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne. Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma...
Hukumar Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA) ta yi kira ga manoma da masu ruwa da tsaki a harkar noma da masu kirkire-kirkire a jihar da su shiga baje kolin noma na kasa da ke tafe. A cikin wata sanarwa da Sashen Kula da Ayyukan Yada Labarai, KNARDA ya fitar, ta bayyana...
Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan baruwanmu a taronsu karo na 19 da ke gudana a birnin Kampala na kasar Uganda a ranakun 15 da 16 ga wannan wata na Oktoban 2025, sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da ake ciki a yankin Caribbean, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Jamhuriyar Venezuela wajen...
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka. Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari...
Shugaban kasar Indonusiya Prabowo Subianto ya sanar da irin ci gaban da aka samu game da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a gaza, kana ya sanar cewa Jakarta a shirye take ta aike da dakarun tabbatar da zaman lafiya, domin nuna irin tsawon lokacin da kasar ta dauka tana nuna goyon bayanta ga alummar...
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da Patrick Herminie wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC a matsayin wata dama ta ci gaba da daukaka dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa manyan matakai da kara kyautatawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)...
Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zuba jari a fannin kayan aikin wanke hannu da kuma ilimin tsafta. Asusun ya kuma ce kaso 35 cikin 100 na makarantu ne kawai ke da kayan wanke hannu na asali, yayin da kashi 8 cikin 100 na ’yan...
Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya...
Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia...
Jagoran ’yan adawa na kasar Kenya kuma tsohon Firaministan kasar, Raila Odinga, ya mutu yana da shekaru 80 a lokacin da yake karɓar magani a ƙasar Indiya, kamar yadda majiyoyin asibiti da ’yan sanda suka tabbatar a ranar Laraba. Rahotanni daga Asibitin Devamatha da ke Kerala, kudancin Indiya, sun ce Odinga ya samu bugun zuciya...
Wasu kudurori guda 3 da ke dauke da bukatun kafa wasu hukumomi 3 sun samu karatu na biyu a zauren majalaisar dokokin jihar Jigawa. Kudurorin guda 3 sun hada da na kafa Hukumar Samar da Hanyoyin Mota a yankunan karkara, da na kafa Hukumar Samar da Kudade Domin Ayyukan Hanyoyin Mota a yankunan karkara da...
Mahaifin margayi Bilyaminu wanda matarsa Maryam Sanda ta kashe, ya ce shi ne ya roki Shugaba Tinubu ya yafe mata duk da hukuncin kisa da kotu ta yanke mata kan laifin. Malam Ahmed Bello Isa ya bayyana haka ne yayin ganawa da ’yan jarida, tare da mahaifin Maryam, Alhaji Garba Sanda. Sun gudanar da taron...
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara. A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude...
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi a Ibadan, a Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar...
Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin...
Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar ba abinda ya faru. Sun kuma bayyana tsagaita wutan da aka samar da Hamas tana tangal tangal saboda tun farko ba’a gina shi kan yadda zata dore ba. Kamfanin dillancin...
Dangin Marigayi Bilyaminu Ahmed Bello sun bayyana takaicinsu bisa sanya matarsa, Maryam Sanda, wadda kotu ta ɗaure ta kan laifin soka masa wuka har lahira, a cikin jerin mutanen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa. A shekarar 2020 ne kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan...
Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin...
Rahotanni sun bayyana cewa an gano daruruwan gawawwaki a karkashin burabutsai a yankin gaza bayan sanar da dakatar da bude wuta tsakanin isra’ila da kuma kungiyar Hamas, adadai lokacin da tawagar agaji ke ci gaba da gano gawarwaki da suka makale a karkashin duwatsu bayan kwashen shekaru 2 Isra’ila na kisan kare dangi, Majiyar Asibiti...
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ASUU ta ƙasa da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen tattaunawa kan buƙatun ƙungiyar. Don haka sun fara yajin aiki daga yau na gargadi na tsawon mako biyu. Ana ta bangaren...
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”. Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana...
Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato kudi fansa kimanin Naira miliyan 5 a yankunan Magumeri da Gajiram a jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanar Sani Uba , ya ce sojojin da suke sintiri a yankunan ne suka hallakan mayakan bayan sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan...
Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe. Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi...