Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
Published: 26th, October 2025 GMT
Ya ƙara da cewa Basira ‘Yar Guda ta bayyana cewa za ta amince da aure ne kawai idan Idris ya mallaki gidansa na kansa, ba wanda yake haya ba. Wannan ne ya sa kotu ta dakatar da yanke hukunci domin bai wa Hisbah damar tabbatar da cewa an bi tsarin aure yadda ya dace da shari’ar Musulunci.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky
Shugaban mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya ce zai yi hisabi da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a gaban Allah kan abin da ya faru a Zariya a 2015.
Rikicin ya fara ne bayan da mambobin IMN sun tare wa tsohon Hafsan Soji, Tukur Buratai, hanya.
Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025 Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a AdamawaLamarin fara a matsayin ƙaramin rikici daga baya ya rikiɗe zuwa babban al’amari, lamarin da ya sanya sojoji buɗe wa mabiyan wuta.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da kwamitin bincike na jihar, sun bayyana cewa an kashe tare binne ɗaruruwan mambobin IMN a asirce bayan faruwar lamarin.
Daga baya an kama Zakzaky da matarsa, an tsare su har zuwa 2021, kafin daga baya kotu ta wanke su.
Bayan cikar lamarin da shekara 10, Zakzaky ya ce gwamnati ta kasa ɗaukar alhakin abin da ya faru.
Ya ce: “Babu abin da aka yi. Ba su yadda cewa wani abu ya faru ba, duk da cewa kwamitin bincike ya miƙa rahotonsa tun 2016.”
Zakzaky, ya kuma zargi gwamnatin yanzu da yin shiru a kan lamarin, duk da alƙawarin da ta yi na duba rahoton da kuma biya iyalan waɗanda abin ya shafa diyya.
Ya ce: “Sun tabbatar mana cewa za su magance batun, amma tun daga lokacin shiru kake ji.”
Da aka tambaye shi ko ya yafe wa Buhari, Zakzaky, ya ce ya bar komai a hannun Allah, kuma zai masa hisabi da shi ranar gobe ƙiyama.
Zakzaky ya ce: “Game da Buhari, za mu gana a Ranar Alƙiyama. Lissafin Buhari ya ƙare.”
Ya ƙara da cewa harin bai yi nasarar daƙile IMN ba, sai ma ƙara ɗaukaka sunan ƙungiyar inda ta yi fice a duniya.
Zakzaky, ya ce sun kai ƙarar lamarin kotun ƙasa da ƙasa, sannan ƙofarsu a buɗe ta ke domin tattaunawa da gwamnati.
Ya ce: “Ko ba sa son ganinmu, za su gan mu. Ko ba sa son jinmu, za su ji mu.”