Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum
Published: 25th, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa a harkar tsaron sararin samaniya, domin hana ’yan ta’adda na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare.
Zulum, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa, bayan wani hari da Boko Haram suka kai.
Sauke Hafsoshin Tsaro: Za a yi wa Janar-Janar 60 ritaya daga aiki ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar ShendamYa ce, “Babban abin da nake son magana a kai shi ne amfani da jirage marasa matuƙa.
Gwamnan ya bayyana cewa yawaitar irin waɗannan jirage a hannun mahara barazana ce ga tsaron ƙasa.
“Dole mu haɗa kai domin magance wannan sabon salo,” in ji shi.
Zulum, ya kuma nemi a ƙara tsaurara tsaro a bakin iyakoki da kuma inganta tsaron sararin samaniya.
A cewarsa: “Wannan abu ne da ya kamata a yi cikin gaggawa, ba tare da ɓata lokaci ba.”
Haka kuma, ya yi kira ga jama’ar jihar da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar kai musu bayanan sirri da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro.
Ya ƙara da cewa: “Mun samu labari cewa za a kai hari a Mafa, kuma mun sanar da hukumomin da ya kamata su sani. Amma ganin yadda abubuwa suka faru, akwai alamun zagon ƙasa, don haka ya kamata a bincika a kuma yi gyara.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Jirage Marasa Matuƙa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC
Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron ƙasa ba zato ba tsammani.
Aminiya ta ruwaito yadda shugaban ƙasa ya sauya hafsoshin tsaron da ya naɗa shekaru biyu da suka wuce.
Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri ’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan NejaA cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce jam’iyyar ta damu ganin yadda aka yi sauyin ba zato ba tsammani bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki.
“Ko da yake shugaban ƙasa yana da ikon yin irin waɗannan sauye-sauye, amma mum damu da wannan mataki biyo bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki,” in ji Abdullahi.
Ya ƙara da cewa amsar da gwamnatin ta bayar game da wannan jita-jitar ba yi cikakken bayani ba face ruɗani da ta jefa mutane a ciki.
ADC ta ce irin wannan sauyi na iya haifar da ruɗani a rundunar sojoji, don haka dole ne a samu dalilai masu ƙarfi kafin a yanke irin wannan hukunci.
Jam’iyyar, ta ce gwamnati tana da alhakin bayyana wa ’yan ƙasa ainahin abin da yake faruwa .
“Mu a matsayin jam’iyyar adawa, muna son zaman lafiya da ɗorewar dimokuraɗiyya a ƙasarmu.
“Abin da ke faruwa a maƙwabtan ƙasashe kamar Chadi da wasu ƙasashen yankin Sahel ya ƙara mana damuwa,” in ji sanarwar.
Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da rashin mayar da hankali, inda ta bayyana cewa matsalar tsaro na ƙara ta’azzara yayin da ’yan ta’adda da ’yan fashi ke sake yin ƙarfi a wasu yankuna na ƙasar.
“Sauya hafsoshin tsaro ba zai warware waɗannan matsalolin ba. Maimakon haka, zai sa mutane su yi zargin cewa gwamnati ta fi mayar da hankali kan siyasa da mulki sama da kare rayukan ’yan ƙasa,” in ji Abdullahi.
ADC, ta gargaɗi gwamnati cewa sauya dukkanin hafsoshin tsaro a lokaci guda na iya ƙara janyo jita-jita da hasashe marasa tushe.
Saboda haka, jam’iyyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fito fili ta bayyana gaskiya, tare da tabbatar wa ’yan Najeriya cewa dimokuraɗiyyar ƙasar ba ta cikin hatsari.