Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan
Published: 24th, October 2025 GMT
Sakatare-Janar na kwamitin hadin gwiwa na yankin Gulf Jassim Al-Badawi ya yi kakkausar suka kan amincewa da wasu kudirori guda biyu a majalisar Knesset ta Isra’ila da ke da nufin kakaba ikon Isra’ila kan yankin yammacin kogin Jordan da ta mamaye.
A rahoton talabijin ta Aljazeera, Jassim Al-Badawi a cikin wata sanarwa a jiya Alhamis ya jaddada cewa, matakin da majalisar Knesset ta Isra’ila ta dauka, wani mataki ne da ya saba wa kudurorin kasa da kasa, da kuma kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi na samun zaman lafiya mai dorewa.
Haka nan kuma ya jaddada cewa ayyukan gina matsugunan da gwamnatin sahyoniyawan suke yi a fili take ga hakkokin tarihi na al’ummar Palastinu da dokokin kasa da kasa ne.
Sakatare-janar na kwamitin hadin gwiwar kasashen yankin Gulf ya yi kira ga kasashen duniya da su sauke nauyin da suka rataya a wuyansu tare da matsa lamba a kan mahukuntan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da wadannan ayyuka masu hadari da kuma kara gurgunta harkokin tsaro da zaman lafiyar yankin.
Al-Badawi ya nanata matsayar kwamitin hadin gwiwa na yankin tekun Fasha na goyon bayan al’ummar Palasdinu da halalcin ‘yancinsu na kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta.
A ranar Laraba, Majalisar Knesset ta Isra’ila ta amince da wasu kudirori biyu: daya na mayar da yankin yammacin kogin Jordan kaco kaf a karkashin ikon Isra’ila, daya kudirin kuma za a hade matsugunan yahudawa na Ma’aleh Adumim da yankunan Falastinawa da ke gabashin birnin Kudus.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domin Kare Kanta October 23, 2025 Jagora: Allamah Na’ini Ya Kasance Ma’abocin Ilimi Da Sanin Siyasa October 23, 2025 Kimanin Bakin Haure 40 Ne Suka Mutu A Kokarin Ketarawa Turai Ta Tekun Mediterranean October 23, 2025 Hamas Tayi Maraba Da Karyata Ikirarin Isra’ila da Kotun Duniya ICJ Tayi Kan UNRWA October 23, 2025 Alkalai Sun Yi Watsi Da Karar Da Yan Adawa Suka Shigar Kan Zargin Magudi A Zaben Kamaru October 23, 2025 Yahudawa A Kasashen Duniya Sunyi Kira Ga MDD Da Ta Kakabawa Isra’ila Takunkumi October 23, 2025 Ministan Leken Asiri: Iran Bata Da Tabbacin Kare Maslaharta A Tattaunawa Da Amurka. October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda
Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na ganin ta kara kusantar sabuwar gwamnatin siriya bayan faduwar gwamantin Bashar Al-Asad.
Gwamnatin birtaniya ta bayyana cewa wannan mataki zai sanya su kara kusanci da gwamnatin siriya da Abu mohammad Al-Jolani ke jagoranta wanda aka fi sani da Ahmed sharaa wanda shi ne shugaban kungiyar Al-Qaida kuma kwamandan Daesh.
Wannan sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen birtaniya David lammy ya kai kasar siriya a watan yuli, wanda ya sanya ya zama shi ne babban jami’in diplomasiya da ya kai ziyara kasar a tsawon shekaru.
Kuma mataki yazo ne duk da hujjoji da ake da su na laifukan yaki, cin zarafin dan adam da kungiyar HTS ta yi musamman ma kan kabilu marasa rinjaye irin su alawiyyawa wanda suke fuskantar gallazawa daga bangaren gwamnati.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci October 21, 2025 An Yi Fashi Da Makami A Gidan Adana Kayan Tarihin ” Louvre” Na Kasar Faransa October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci