Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu
Published: 26th, October 2025 GMT
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.
Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.
Gwamna Raɗɗa wanda ya ce gwamnati da ta kafa cibiyoyi da dama a Jihar Katsina domin kula da kayan sawa da sarrafa abinci da sauran su, kuma gwamnati a shirye take domin farfaɗo da masana’antu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kaduna Tare Da AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma
Ya ƙara da cewa Kaduna ita ce jihar da ta cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma.
Shugaban AUDA–NEPAD a Nijeriya, Honarabul Jabir Abdullahi Tsauni, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da suka bai wa shirin damar faɗaɗa zuwa dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar.
A cewar Tsauni, an horar da ƙanana manoma 345 kan kyawawan hanyoyin noma da kuma dabarun noma masu jituwa da yanayin sauyin yanayi, ciki har da noman lambu na gida irin su tumatir, barkono mai zaƙi, masara, wake, da waken soya.
Komashinan noma na Jihar Kaduna, Murtala Dabo, ya bayyana cewa wannan shiri ya nuna yadda Kaduna ke da niyyar mayar da noma a matsayin sana’ar da ke kawo riba, ba kawai hanyar rayuwa ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA