An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Published: 26th, October 2025 GMT
A yau Asabar 25 ga wannan wata, ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar sun gudanar da liyafar murnar kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, a dakin taro na Diaoyutai dake birnin Beijing.
Direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Song Tao ya yi jawabi a gun liyafar cewa, an kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan a yayin cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin, wanda babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ya gabatar, kuma zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar ya yi bincike tare da zartas da batun bisa dokoki, kuma wannan ya biya bukatun jama’ar kasar Sin da cimma burin dukkan kasar baki daya.
Kebe wannan rana, muhimmin aiki ne ga kasar Sin wajen tunawa da tarihin kasar da jaruman da suka ba da gudummawa ga kasar, da kuma sa kaimi ga tabbatar da ka’idar Sin daya tak a duniya, da kin amincewa da ‘yan aware na yankin Taiwan da masu tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin, da kuma nuna goyon baya ga bangarori masu kaunar kasa da neman dinkuwar duk kasar Sin. Muna da karfi wajen yaki da ‘yan aware na yankin Taiwan, da sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan.
Ya kara da cewa, muna son zurfafa mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin gabobin biyu, da raya al’ummar kasar Sin baki daya. Hakazalika, mun yi imani da sa kaimi ga samun dinkuwar duk kasar Sin, da kawo moriya ga jama’ar yankin Taiwan. Muna da karfi wajen tinkarar kalubale, da yin kokarin cimma burin farfadowar al’ummar kasar. (Zainab Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na a yankin Taiwan da
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato
Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan manoman da suke aikin girbin amfanin gona a yankin Mbor na masarautar Mushere na Ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyu a ranar Laraba da yamma.
Shugaban Ƙungiyar matasan Mushere, Kopmut Monday ne ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zangaA cewar shugaban matasan, ’yan bindigar sun kai farmaki wurin ne inda suka buɗe wuta kan manoman da ke cikin aikin girbin amfanin gona, inda ya ce manoman sun tsere domin tsira da rayukansu.
Shugaban ya zargi makiyaya da kai wa mambobinsu hari, inda ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin “mazauna garin Rongjing ne a jiya da yamma sun kai wa ’yan ƙungiyarmu hari a yankin Mbor a lokacin da suke girbin amfanin gona, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku da jikkata mutum biyu da harbin bindiga. Waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
Monday yya ƙara da cewa, al’ummar yankin suka sha fama da irin wannan hari a ranar 26 ga watan Mayu an kashe mutane bakwai.
Ya ce “lamarin baya-bayan nan wani mummunan al’amari da ya faru a watan Mayu, wanda ya yi sanadin kisan mutane bakwai, da jikkata wasu da kuma ƙona gidaje da dama ciki har da coci guda biyu.”
Monday ya kuma bayyana cewa, al’ummar da aka kai wa harin baya-bayan nan, sun yi kira ga jami’an tsaro da su tura isassun ma’aikata don dawo da zaman lafiya a yankin saboda mazauna yankin ba za su iya gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba.