Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15
Published: 24th, October 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15, da ke da nufin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.
এছাড়াও পড়ুন:
Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara.
Yayin da yake bayyana dalilin sauya sheƙar, Amaewhule ya ce sun bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin jam’iyyar.
Bugu da ƙari, a wani mataki da ake ganin na ƙoƙarin kaucewa gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 daga Gwamna Siminalayi Fubara ne, Kakakin ya sanar da dage zaman majalisa har zuwa watan Janairu 2026.
Ayyukan majalisar a kwanakin baya-bayan nan sun nuna cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare ba tsakanin bangaren zartarwa da majalisar jihar.
A watan Maris 2025, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamna da majalisa wanda kusan ya jawo rugujewar tafiyar da mulki a jihar.
Shugaban ƙasa ya kuma tsige Gwamna Fubara, mataimakinsa da kuma dakatar da majalisar jihar.
Sai dai an dawo da gwamnan da ’yan majalisar a jihar bayan an ɗage dokar ta-bacin a watan Satumba, tare da fatan cewa zaman lafiya ya dawo tsakanin bangarorin biyu.