Farfesa Muhammed Khalid Othman Ya Zama Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Ta Dutsinma
Published: 26th, October 2025 GMT
Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta zabi Farfesa Muhammed Khalid Othman a matsayin sabon Shugaban Jami’ar na dindindin, tare da amincewar Majalisar Gudanarwar Jami’ar.
Da yake zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, Magatakardar Jami’ar, Dokta Musa Ajiya, ya bayyana cewa mai kula da jami’ar (Pro-Chancellor), Ali Abubakar-Jatau, ne ya sanar da nadin.
A cewar Dokta Ajiya, Abubakar Jatau wanda shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa, ya bayyana hakan ne bayan taron na musamman karo na 36 da aka gudanar a daren Juma’a.
Ya ce Farfesa Othman ya fito ne a matsayin wanda ya fi kowa cancanta bayan wani tsari na tantancewa mai tsauri kuma bisa gaskiya, a cikin mutane 17 da suka nemi mukamin 17.
Ya ƙara da cewa an gudanar da tsarin tantancewa cikin gaskiya, inda aka mika sunayen ‘yan takara uku mafi cancanta don tantancewa da amincewar Majalisar Gudanarwa.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, Farfesa Othman ya fara aiki daga matsayin Mataimakin Malamin Jami’a har zuwa matsayin Farfesa, inda ya riƙe matsayi daban-daban a matsayin malami, mai bincike, da kuma mai gudanarwa.
Haka kuma, ya taɓa zama Darakta-Janar na Hukumar Nazarin Ingantaccen Aikin Noma ta NAERLS da ke Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Yanzu haka Farfesa Othman memba ne a Majalisar Gudanarwar Jami’ar, inda yake wakiltar Majalisar Dattawan Jami’ar.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Shugaban Jami ar Dutsinma
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato
Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan manoman da suke aikin girbin amfanin gona a yankin Mbor na masarautar Mushere na Ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyu a ranar Laraba da yamma.
Shugaban Ƙungiyar matasan Mushere, Kopmut Monday ne ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zangaA cewar shugaban matasan, ’yan bindigar sun kai farmaki wurin ne inda suka buɗe wuta kan manoman da ke cikin aikin girbin amfanin gona, inda ya ce manoman sun tsere domin tsira da rayukansu.
Shugaban ya zargi makiyaya da kai wa mambobinsu hari, inda ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin “mazauna garin Rongjing ne a jiya da yamma sun kai wa ’yan ƙungiyarmu hari a yankin Mbor a lokacin da suke girbin amfanin gona, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku da jikkata mutum biyu da harbin bindiga. Waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
Monday yya ƙara da cewa, al’ummar yankin suka sha fama da irin wannan hari a ranar 26 ga watan Mayu an kashe mutane bakwai.
Ya ce “lamarin baya-bayan nan wani mummunan al’amari da ya faru a watan Mayu, wanda ya yi sanadin kisan mutane bakwai, da jikkata wasu da kuma ƙona gidaje da dama ciki har da coci guda biyu.”
Monday ya kuma bayyana cewa, al’ummar da aka kai wa harin baya-bayan nan, sun yi kira ga jami’an tsaro da su tura isassun ma’aikata don dawo da zaman lafiya a yankin saboda mazauna yankin ba za su iya gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba.