2025-09-17@20:32:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 28
«a Kannywood»:
Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan da aka kafa masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da su. A cikin wannan tattaunawar, ya bayyana cewa bai taɓa yin da-na-sanin shigarsa sana’ar ba, sannan ya bayyana dalilin da yanzu ba a cika ganin sa sosai a fina-finai ba, da ma yadda ya ce fim ɗin Hausa ya taɓa zama silar sasanta wasu ma’aurata da aurensu yake tangal-tangal. Tun yaushe ka shiga harkokin fim ɗin Hausa? Ai harkar fim ɗin Hausa daga baya ta fito, a da wasan kwaikwayo ake yi. Na fara wasan kwaikwayo na rediyo wajen 1970, lokacin ina ƙarami. A lokacin rikoda ta fito. To a sannan na fito a matsayin mace...
Na dauki fim sana’a, kuma sana’ar ce. Dan wallahi sana’a ce me kyau ma, ta ba ni gida, ta ba ni mota, na ci, na koshi. Yanzu idan zan shekara na ce ba zan fita ba, a cikin gidana ne, kuma darajar Kannywood. Ina finafinai na a haka na samu gidana, na gina gidan kuma nake zaune cikinsa. Ko kina da ubangida, a cikin masana’antar Kannywood? Ai ni a masana’antar duk wani sa’a na, ko wanda ya girmen ubangidana ne, ni ba butulu ba ce da zan ce ban da iyayen gida. Ana rade-radin akwai yaranki a cikin masana’antar Kannywood, mene ne gaskiyar maganar? ‘Ya ta guda daya ce take Kannywood, saboda da kanta ta ce “Umma ina...
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a garin Kano a Bichi LGA, na yi firamare a Bichi ‘Chiranci Primary School’. Amma ban cigaba ba da yake mu fulani ne, daga nan aka yi min aure. Bayan na fita daga gidan mijina, sai na fara koyan wasan dabe (Drama), daga nan ne dai na samu kaina a cikin wannan sana’ar. Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim? Abin da ya ja hankalina har na fara fim, bayan na yi aure na auri dan fim, Allah ya ji kanshi Rabilu Musa (Ibro). Bayan na fita daga hannunsa kawai sai na yi sha’awar ni ma na fara fim. To, akwai wacce nake so...
Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A. Zango ya agwance da jaruma Maimuna Musa. Marubuciya a masana’antar, Fa’iziyya D. Sulaiman ce ta sanar da auren nasu a wani rubutu da ta wallafa a Facebook. Wani mutum yanke makazutarsa a Borno Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025) Auren dai ya zo cikin bazata, domin babu wanda ya san da neman sai labari aka ji jaruman sun shiga daga ciki. Jaruma Maimuna matashiya ce wadda tauraronta ya fara haskawa a Kannywood. Ta yi fina-finai kamar Kwana Casa’in, Garwashi da sauransu. A baya-bayan nan ma fitacciyar jaruma a masana’antar, Rahama Sadau, ita ma ta yi aure, lamarin da ya bai wa mutane da dama mamaki.
Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana ba, koda kuwa da wasa, in ji shi. Mai Dawayya ya buƙaci matasan mawaƙa masu tasowa a masana’antar ta Kannywood, da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu, duniya kuma take yi da su; wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba. An ɗaura auren a ranar Asabar a Masallacin da ke Unguwan Rimi, a Jihar Kaduna, bayan Ibrahim ya biya sadaki Naira 300,000. Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara Rahama, ta sanar da ɗaurin auren a shafinta na Facebook, inda ta gode wa Allah tare da neman addu’a daga masoyanta. Ta bayyana farin ciki da godiyarta, tare da fatan wannan sabon babi na rayuwarta zai kasance mai albarka. Auren mata na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar mahaifinta, Ibrahim Sadau. ’Yan uwanta sun yaɗa hotuna da bidiyon bikin a kafafen sada zumunta, inda...
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya yi nuni da cewa; yanzu mafi akasarin mutane, ba sa son abin da zai taimaka musu; kawai dai sun fi mayar da hankali wajen sharholiya iri-iri. da yake amsa tambaya a kan me yasa ya fi mayar da hankali wajen ɗora bidiyo, musamman na jarumai mata a Masana’antar Kannywood a shafukansa na sada zumunta, musamman kuma ‘Facebook’? Sai Baba Sadiƙ ya ce; ba komai ba...
“Ni na san fina-finan da aka haska a gidajen Gala da aka samu fiye da Naira miliyan daya a rana daya, wasu kuma har miliyan biyu, yanzu idan ka duba tun daga Kano har Nijar za ka dinga ganin gidajen Gala, haka zalika daga nan Kano har zuwa birnin Legas ma akwai su, saboda haka; me zai hana mu rika amfani da wannan dama wajen fadada adadin kudaden shiga da wannan masana’anta mai albarka take samu? Daga karshe, ya bukaci hadin kai daga dukkanin wasu masu ruwa da tsaki, wajen ganin wannan haka ya cimma ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi a kansu. Aminiya ta rawaito cewa hatsaniyar ta samo asali ne bayan fitattun ‘yan Kannywood da suka hada da Abdul M Sharif, Nura M Inuwa, Abubakar Bashir Maishadda, Sadik Sani Sadik, da sauransu suka kai wa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar ziyarar goyon baya. Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba Wannan ya tunzura Alhikma kasancewar wasu daga cikin wadanda suka je mubayi’ar ‘ya’yan kungiyar YBN ne a baya, da kuma 13/13 ta ubangidansa, mawaki Rarara. A cikin wadanda Alhikima...
Har ila yau, Maishaddar ya ci gaba da bayyana cewa; dangane da batun da mutane ke yi na cewa, alaka tsakaninsa da jarumi kuma mawaki Umar M. Sharif ta yi tsami, duba da cewa; an daina ganinsa a ci gaban shirin ‘Gidan Sarauta’ da Maishadda ke daukar nauyi, Bashir ya bayyana cewa; wannan magana ko kusa babu kamshin gaskiya a ciki, don ba a ga Umar a shirin ‘Gidan Sarauta’ zango na 4 ba, wannan ba dalili ne da zai sa a yi tunanin ko akwai wata matsala a tsakanina da shi ba, domin kuwa; a duk wani shiri mai dogon zango, akwai lokacin da za a daina ganin jarumi, amma kuma daga baya ya sake bayyana. Bashir ya kara...
A ranar Juma’a, 25 ga watan Afrilun shekarar 2025 ce aka daura auren Dauda Kahutu Rarara da amaryarsa Aisha Ahmad wadda aka fi sani da Aisha Humaira a birnin Maiduguri da ke Jihar Borno, an dade ana rade-radin akwai soyayya tsakanin ma’auratan biyu, amma a duk lokacin da aka tambaye su, sai su ce aiki da ne ya hadasu ba wani abu ba. A shekarar da ta gabata Rarara ya rera wata waka mai taken ‘Aisha’, wadda a ciki ya baza kalaman soyayya har aka yi ta cewa da ita yake yi, amma sai aka yi amfani da wakar a fim din da ita jarumar ta shirya mai suna ‘A cikin biyu’ wanda Ali Nuhu ya hau a matsayin mijinta...
Sai kaga mutum daga ya samu wata yar dama to do yake ace ya samu wata hanyar wulakanta wannan wanda yayi masa rana kokuma ya wuce shi a matsayi ko wani abin Duniya ba tareda la’akari da cewar wannna wanda ya koya maka to ya fika sanin komai a wannan harkar musamman ma a nan masana’antar Kannywood. Don haka kamata ya yi ce mutane sun fahimci cewar babu ta yadda za a yi ka ci gaba matukar ka na da wata niyyar cin amanar wanda ya taimake ka ka kai wani matsayi na rayuwa, ni yanzu a matsayina na Ayatullahi Tage na yi biyayya ga maigidana Alhaji Tage wanda ya nuna mani hanya, ya rike ni kamar dan da ya...
Maryam Abubakar, ɗaya ce daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ’yan ƙalilan da suka yi nasarar bin sahun iyayensu a harkar fim. Matashiyar jarumar, wadda aka fi sanin ta da Maryam Intete a masana’antar, ta yi bayani a kan matsayinta na wadda iyayenta suka suka a cikin cikin harkar fim. Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A wannan tattaunawar, jarumar ta yi bayani game da gogewarta da yadda ake samun daukaka a Kannywood, da wasu abubuwa game da ita kanta da iyayenta, da kuma sana’ar fim da dai sauransu. Wace ce Maryam Abubakar? An haife ni ne a Kano kuma a nan na girma....
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani nazarin finafinan Kannywood da BBC Hausa ta gabatar ya nuna cewa, Masana’antar Kannywood tana ta samun sauye-sauye, musamman a bangaren shirya fim da kasuwancinsa, inda daga CD aka koma sinima, yanzu aka koma YouTube, sannan ake ta hankoron shiga manhajojin duniya ka’in da na’in. A wannan shekarar, kamar kowace shekara, masu shirya finafinan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da fitar da finafinai masu kyau, wadanda suka kayatar da masu kallo. Yadda Kanawa suka huce takaicin rashin Hawan Sallah Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2) Tun bayan komawa dora finafinai a YouTube, yanzu za a iya cewa harkokin Kannywood sun fara komawa yadda suke a baya, bayan a baya masana’antar ta fara durkushewa. Nazarin...
A yayin hirar Abdullahi Shuaibu ya ce “Ni dai suna na Abdullahi Shuaibu, amma al’uma na kirana da Karkuzu, ko kuma Abdullahi Kano, yanzu shekaru 43 kenan ina wannan harka ta fina finan Hausa, amma yanzu wasu lokutan sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na, kuma wani abin tausayi, ni Karkuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da nake ciki an sa shi a kasuwa, ba gida na ba ne, haya nake yi. Ya ci gaba da cewa, yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, in an ce na mallaki gida mai dimbin yawa, wadansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne, amma wallahi tallahi,...
Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki. Me ya sa ba a gamawa din? BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallon shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba. Ya ce kasancewar Youtube ya dade kudu, amma bai je arewacin Nijeriya ba ne ya sa su ka gwada domin su koya wa mutanen arewa kallon fim a YouTube, shi kuma wannan fim din ya na ciki, ko in ce shi ne daya...
Daraktan Fim ɗin Mai martaba, Prince Daniel (ABOKI), ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa yana fuskantar tsangwama a Kannywwod saboda bambancin addininsa. A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Aboki ya ce shi ma batun cewa ana nuna masa bambamci a Nollywood saboda ɗan arewa ne ba shi da tushe balle makama. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku “Wasu labarai da aka wallafa na nuna cewa wai masana’antar Kannywood ta ƙi amincewa da ni saboda addini na, ita kuma Nollywood saboda ni ɗan Arewa ne. “Da farko dai ban yi hira da wata jarida...
A yanzu nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara. Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram. SShi ma dai fitaccen jarumin Kannywood kuma Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu, ya wallafa hoton marigayi Ƙarƙuzu a shafinsa na Facebook yana mai roƙon Allah Ya jikansa. Ƙarƙuzu dai tsohon jarumi ne a masana’antar Kannywood da ya yi tashe tun a shekarun 1980. Ana iya tuna cewa wata hira da ya yi da Zinariya TV kuma Mujallar Fim ta wallafa a shekarar 2023, Ƙarƙuzu...
Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood. Mene ne tarihinki a takaice? To ni ‘yar asalin garin Kano ne. An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano. Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano. Ke nan kin taɓa yin aure? Eh na taɓa yin aure,...
Masana’antar Kannywood ta dade tana nishaɗantar da al’umma, musamman Hausawa da sauran kabilun Arewacin Najeriya. A makon jiya Aminiya ta ruwaito a cewa kasuwancin fina-finan ya samu koma-baya matuƙa, wanda hakan ya sa wasu suke nuna yatsa ga furodusohin yanzu kan gaza shirya fim ɗin da za a iya haskawa a Netflix da sauran manyan hanyoyin nuna fina-finai da za su samar wa masana’antar kuɗin shiga. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza Wannan ya sa Aminiya ta yi waiwayen wasu furodusohin da aka daina jin ɗuriyarsu a masana’antar. Salisu Galadanchi – Shi ne Daraktan Fim din Turmin Danya, fim na farko a Kannywood, ya...
Abinda ya sa nike fatan ganin na zama gwamna shi ne saboda banida wani burin da ya wuce in ga cewar matsalar tsaro ta kau a Nijeriya musamman Arewacin kasar inda wasu ke wasa da rayukan al’umma saboda wata bukata ta kashin kansu, wasu tsiraru na amfani da rayukan mutane a matsayin kasuwanci ko kuma don neman daukaka ya kara da cewa. A ci gaba da hirar Sadik ya amsa tambayar da aka yi mashi a kan fina-finan da yayi da kuma wadanda yake kallo a matsayin wanda yafi so a cikinsu, inda ya ce daga cikin fina-finan da ya fito wadanda kuma yafi so, akwai Mati Da Lado sai kuma wani fim mai suna Dan Marayan Zaki. Abinda ya...
Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba wani kudin azo a gani suka bayarwa ba, yanzu idan fim dinka bai kai matsayin shiga tashar NETFLID ta kasar Amurka ba, ba lallai ne ya kai inda kake bukata ba inji shi. Ya ci gaba da cewa hakan yasa nike bayar da shawara wajen ganin mun fadada tunaninmu wajen zakulo wasu sabbin hanyoyi da zamu dinga fitar da fina finanmu zuwa inda ya kamata...
Amma duk da haka, hatta wake-wake da raye-raye da kuma abinda ya shafi sinima, tsofaffin jarumai ne su ka kawo su a masana’antar Kannywood, saboda haka ya kasance wani lokaci mai ban sha’awa a tarihi lokacin da Hamisu Lamido Iyan-Tama ya hadu da Hindatu Bashir a kan dandamali don ba shi lambar yabo. Dukkanmu sai muka tuna da fim dinsu na Badakala (wanda wani jarumi Bashir Mudi Yakasai ya shirya), inda suka yi fim mai dauke da rawa da waka na farko a cikin fina-finan Hausa,wato a shekarar 1997 wannan fim ya daga abinda yanzu ake kira Hausa Afropop, domin shi ne wakar fina-finan Hausa ta farko da aka kai wa Rabi’u BK a kasuwar Kofar Wambai domin sayar da...
Daga karshe, jarumin wanda ya shafe shekaru fiye da 10 a Masana’antar Kannywood, ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim, su tabbatar sun zama masu hakuri da biyayya ga na gaba da su, muddin suna son samun nasara a rayuwarsu ta jarumai. “Dole ne ka kasance mai hakuri a rayuwa, domin kuwa babu wanda ya zama wani abu ba tare da ya sanya hakuri a cikin al’amuransa na yau da kullum ba, duk wanda ka gani ya zama wani abu, ko ya samu wata daukaka ko shahara a rayuwa, to dole akwai kalubalen da ya fuskanta, domin kuwa ko a makaranta sai an ware wani lokaci da za a yi jarrabawa; domin gane masu fahimta da wadanda ba sa...
A watan Janairun wannan shekara ta 2025, an fara fitar da sabbin fina-finan Hausa masu dogon zango sama da 10, wadanda ake nunawa a tasoshin ‘YouTube’ daban-daban, bayan wasu da yawa da aka kwana biyu ana haskawa ta kafar. Manyan fina-finai, musamman masu dogon zango da kamfanin Saira Mobies ke daukar nauyi, mai suna Labarina; na daga cikin fina-finan da ke kan gaba a ‘YouTube’, harkokin fina-finan Kannywood, sun koma wannan kafar ne; tun bayan da tattalin arzikin masana’antar ya tabarbare sanadiyar mutuwar kasuwar CD, sai ake tunanin komawa ‘YouTube’ din zai inganta kasuwancin masana’antar kamar yadda yake a baya. An dade ana shirya fina-finan Hausa masu dogon zango, amma fim din Izzar So, na Lawan Ahmad; na cikin wadanda...
A zamanin baya, duk da cewa fina-finan nanaye sun fi karbuwa a wajen mutane, amma haka muke kokartawa wajen ganin an shigar da wata koyarwa ta addinin musulinci ko kuma wani abu mai amfani da zai amfanar da al’umma ta wani bangare, amma yanzu duk an daina wannan, masu shirya fina-finai na amfani da labarai masu tsafta da amfanarwa, ba tare da da sanya wakoki ko makamantansu a ciki ba, in ji Malam. “Dalili kuwa shi ne, yanzu ‘ya’yan mutunci da arziki su ne ke yin harkar, sannan kuma su ne suke samun arzikin duniya da na lahira, akwai lokacin da har mata masu zaman kansu din, sai da muka daina samun su idan zamu yi fim, amma yanzu wannan...
Har ila yau ya ce, idan aka yi maganar mukaman da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka bai wa wasu daga cikinmu, ba yana nufin cewa; an taimaki masana’antar ba ne, domin kuwa; mafi yawancin wadanda suka samu wadannan mukamai, babu wani ci gaba ko hobbasa da suka yi wajen ciyar da Masana’antar Kannywood gaba. Musa ya ce, illa kawai dai suna taimakon kansu da kuma na kusa da su, wanda kuma ba haka ya dace a ce suna yi ba, dalili kuwa shi ne, har yau babu wani daga cikin masana’antar tamu da ya taba samun wani mukamin gwamnati, ya taimaka wa ita kanta masana’antar, illa kalilan daga cikinmu. A bangaren abokanan fada kuwa a Masana’antar Kannywood, Mai Sana’a...