Zanga-Zangar Miliyoyi A Yemen Ta Jaddada Alkawari Ga Shahidai Da Ci Gaba Da Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu
Published: 17th, October 2025 GMT
Zanga-zangar miliyoyin mutane a birnin Sana’a na sabunta alkawarin da aka yi wa shahidai tare da tabbatar da shirin tallafawa Falasdinu
Babban birnin kasar Yemen, Sana’a, ya halarci wani tattaki na miliyoyin mutane a yau Juma’a mai taken “Shekaru biyu na bayar da gudummawa… da aminci ga jinin shahidai”, tare da tabbatar da gwagwarmaya na goyon bayan al’ummar Falastinu tare da sabunta alkawarin bin tafarkin shahidai da azama.
Daruruwan jama’a a dandalin Al-Sabeen a lokacin tattakin bayar da amana ya kunshi zurfafa fahimtar al’amuran al’umma. Sun yi nuni da cewa al’ummar Yemen duk da killacewar wuce gona da iri, amma suna nan a fagagen alfahari da daukaka, da tsayin daka kan tafarkinsu na imani da jihadi.
Daruruwan mutane daga cikin miliyoyin ne suka daga tutocin kasar Yemen da na Falasdinu, da kuma hotunan Shahidan gwagwarmaya misalign Manjo Janar Mohammed Al-Ghamari da shugabannin shahidan da suka hau kan hanyar Qudus. Sun kuma rera taken da ke tabbatar da shirye-shiryensu na tunkarar makiya yahudawan sahayoniyya idan har suka dawo da kai farmaki kan Gaza da al’ummar Falastinu ta hanyar karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Sun nuna alfahari da girmamawa ga irin gagarumin sadaukarwar da aka bayar na goyon bayan al’ummar Falastinu da ‘yan uwansu a Gaza tun bayan kaddamar da harin “Ambaliyar Al-Aqsa” da kuma girmama shahidan da suka tashi tsaye wajen kare kasarsu da martabarsu da mutuncinsu da kuma tsarkakar Musulunci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yemen Ta Sanar Da Nadin Sabon Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Kasar October 17, 2025 Iran Tayi kira Da A Warware Rikici Tsakanin Afghnistan Da Pakistan Ta Hanyar Diplomasiya October 17, 2025 Hizbullah: Amurka ِDa Isra’ila Ba za Su Iya Yin Nasarar Akanmu ba. October 17, 2025 Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin sabon Shugaban INEC October 17, 2025 Shugaban Kasar Sudan Yana Ziyarar Aiki A Kasar Masar October 17, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Hrin Wuce Gona Da Iri Na HKI October 17, 2025 WSJ: Amurka Tana Tara Rundunonin Yaki A Zagayen Kasar Venezuela October 17, 2025 Shugabannin Kasashen Amurka Da Rasha Za Su Hadu A Kasar Hungary October 17, 2025 Larijani ya isar da sakon Ayatullah Khamenei ga Putin a ziyarar da ya kai Rasha October 17, 2025 Madagaska : Ranar Juma’a za’a rantsar da Kanar Randrianirina October 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Putin Na Rasha Ya Ce; Kasarsa Da India Za Su Kara Girman Kasuwancinsu
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin wanda ya kai ziyarar aiki kasar India ya bayyana cewa kasar tasa da kuma abokiyar kawancenta India za su bunkasa kasuwancinsu.
Ziyarar ta shugaban kasar Rasha a Indiya, tana a karkashin taron da kasashen biyu suke yi ne daga lokaci zuwa lokaci wanda wannan shi ne karo na 23 da ya kunshi ayyukan tattalin arziki, siyasa da al’adu.
A yayin taron, kasashen biyu sun cimma matsayar bunkasa girman kasuwancinsu da zai kai dalar Amurka biliyan 100 daga nan zuwa 2030.
A nashi gefen Fira ministan kasar India, Modi ya ce, duk da fadi tashin daake samu,amma alakar kasashen biyu India da Rasha tana nan daram.
Taron na kasashen biyu dai ya damu Amurka tana mai zargin India da cewa tana taimaka wa Rasha da kudaden da take tafiyar da yakinta na Ukirania.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Na’im Kassim Ya Yi Suka Akan Shigar Kasar Cikin Kwamitin Tattaunawa Da “Isra’ila” Kai Tsaye December 6, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda December 6, 2025 Limamin Tehran: Idan Abokan Gaba Su Ka Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci