Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Published: 26th, October 2025 GMT
A baya bayan nan, kundin da aka amince da shi yayin cikakken zama na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, ya tanadi tsare-tsaren musamman na fadada bude kofofin kasar ga sassan waje, da dora muhimmancin gaske ga samar da sabon yanayin hadin gwiwar cimma moriyar juna.
A halin yanzu, a hannu guda ana ganin zurfafar sabon zagayen juyin-juya-halin fasahohi, da sauyi a ci gaban masana’antu, a gabar da duniya ke bukatar bude kofa da rarraba gajiya sama da duk wani lokaci a baya.
A wannan yanayi mai sarkakiya da duniya ke ciki, Sin ta nacewa kara fadada bude kofofinta, tana kuma ci gaba da karkata akalar nasarorinta kan turbar zamanantarwa ta Sin zuwa tsarin samar da gajiya ga ci gaban duniya na bai daya.
Shaida ta hakika ta nuna cewa, ba zai yiwu a raba tsakanin ci gaban Sin da na duniya baki daya ba, kana ba za a iya raba ci gaban duniya da na kasar Sin ba. Don haka, jigon samar da karin gudummawar Sin ga ci gaban tattalin arzikin duniya na da nasaba da babban tsarin bude kofofi daga mabanbantan sassa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya
Kungiyar ‘yan wasan kokawar Iran na gargajiya na matasa ‘yan kasa da shekaru 23, ta lashe kambun duniya bayan da ta samu lambobin yabo mafi yawa.
Kungiyar ta Iran ta sami lambobin zinariya 3, da azurfa 1 da kuma tagulla 2.
‘yan wasan da Iran da su ka sami kyautar zinariyar sun hada Iman Muhammadi mai ajin nauyi kilio 72, da Gulam Ridha Farakhi mai ajin nauyi kilo 87 da kuma Fardin Hidayati mai ajin nauyi 130.
Wanda ya sami azurfa kuwa shi ne Sajjad Abbaspur mai ajin nauyi kilo 60, sai kuma wadanda su ka sami tagulla da su ne Ahamd Ridha Muhsin Najad mai ajin nauyi 67,sai Abul Fadal Muhmadim ai ajin nauyi 82.
Kungiyar ta Iran ta zama ta daya da daraja 143, yayin da kungiyar kasar Ukiraniya ta zama ta biyu da maki 96, sai kasar Azerbaijan da maki 93.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Iran take zama zakara a fagen kokawar gargajiya ba, domin ta zo na daya a shekarun 2022 da 2024. A shekarar 2023 kuwa an hana ‘yan wasan kokawar na Iran izinin shiga kasar Albania ne.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domin Kare Kanta October 23, 2025 Jagora: Allamah Na’ini Ya Kasance Ma’abocin Ilimi Da Sanin Siyasa October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci